fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Tsaro

Ku zauna damu ayi maganar kafa kasar mu ta Biafra salin Alin>>Nnamdi Kanu ga gwamnatin tarayya

Ku zauna damu ayi maganar kafa kasar mu ta Biafra salin Alin>>Nnamdi Kanu ga gwamnatin tarayya

Tsaro
Shugaban kungiyar dake fafutukar kafa kasar Biafra,  Nnamdi Kanu ya soki gwamnatin tarayya bisa kama Nastura Ashir, wanda ya jagoranci zanga-zangar lumana a Katsina kan Kashe-kashen da ake samu.   Yace saboda menene za'a kamashi dan kawai ya nuna rashin jin dadin kisan da akewa 'yan uwansa? Yace irin abinda ke faruwa fa kenan a kasashen Amurka da Turai. Ya bayyana cewa su dama sun fadi haka zata faru saboda mulkin zalincin dake faruwa a Najeriya,  ya kuma yi gargadin cewa idan ba'a kiyaye ba to Har Sakkwato sai lamarin ya shiga inda zai kara munana.   Yace samun saukin wannan lamari shine a zauna dasu ayi Sulhu.
Bidiyon Yanda Boko Haram suka kai hari garin me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Babagana Monguno:Sun kona Tankokin yakin sojin Najeriya 3

Bidiyon Yanda Boko Haram suka kai hari garin me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Babagana Monguno:Sun kona Tankokin yakin sojin Najeriya 3

Tsaro
A makon daya gabatane Mayakan Boko Haram suka kai hari garin Monguno dake jihar Borno inda nan ne mahaifiyar me baiwa shugaban kasa shawara kan tsaro, Janar Babagana Mungono me murabus.   Bidiyo ya nuna yanda Boko Haram suka kai hari garin tare da lalata Tankokin yaki 3 da ga dukkan alamu Sojoji suka gudu suka bari.   Rahotanni daga baya dai sun bayyana cewa sojojin Najeriya sun kori Boko Haram daga garin inda kuma hari ta sama ya lalata wasu motocin yakin kungiyar da kuma kashe da dama daga ciki, wanda hedikwatar tsaro tace sun kai 20.   A yayin harin, Boko Haram/ISWAP sun so yin amfanibda wani salon Bam da ake cika mota dashi wanda a turance akewa lakabi da Vbied.   Kalli bidiyon a kasa:
Gwamnonin Arewa sun dauki sabbin matakai da zasu magance matsalar tsaro

Gwamnonin Arewa sun dauki sabbin matakai da zasu magance matsalar tsaro

Tsaro
Kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) ta kafa kwamiti wanda ya hada yan bijilanti, mafarauta da kungiyoyin al'umma kan taron tattara bayanan sirri, saurin amsawa da ci gaba da sanya ido a yankin. Shugaban kuma gwamnan Filato, Simon Lalong ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da kakakin sa, Makut Macham ya fitar ranar Juma’a a garin Jos. Aikin wani bangare ne na kudirin Gwamnonin Arewa yayin wani taron wayar tarho da aka yi ranar alhamis. Kwamitin zai kuma yi shawara da shugabannin gargajiya da na addini da na shugabannin yankin na Arewa, don karfafa hadin kansu a kokarin shawo kan matsalolin tsaro. Kwamitin da ke kan tsaron, wanda gwamnan Kogi, Yahaya Bello zai jagoranta, an kuma kafa don inganta hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro wajen aiwatar da matakan tsaro a yankin. Ta...
Da Dumi-dumi: Yan bindiga sun sace mahaifin tsohon gwamnan Filato, Joshua Dariye

Da Dumi-dumi: Yan bindiga sun sace mahaifin tsohon gwamnan Filato, Joshua Dariye

Tsaro
Yan bindiga sun sace Defwan Dariye, mahaifin Joshua Dariye, tsohon gwamnan jihar Filato. Wannan shine karo na biyu da aka sace Defwan. An taba yin garkuwa da shi a gidansa da ke Filato, a cikin Fabrairu 2015. Daga baya jami'an tsaro suka kubutar da shi a kan iyakar Nasarawa / Plateau. An ce yan bindigar sun kai hari gidan shi dake a karamar hukumar Bokkos da ke jihar a ranar alhamis din nan kuma suka yi awon gaba da shi. Kakakin rundunar yan sandan jihar Ubah Ogaba, ya ce an tura jami’an tsaro zuwa yankin kuma za su bi bayan mutanen da suka sace shi tare da tabbatar da ansake shi. “Bayan da muka samu labarin, kwamishinan yan sanda ya jagoranci sauran jami’an zuwa Bokkos. An tura Jami'an tsaro don subi bayan wadanda suka sace shi kuma muna fatan za a sake wanda aka ...
Hotuna:Yanda Matasa suka kwace Bindigar dansanda saboda ya karbi cin hanci

Hotuna:Yanda Matasa suka kwace Bindigar dansanda saboda ya karbi cin hanci

Tsaro
Jami'an 'yansanda sun karbi bindigar AK47 da wasu matasa suka kwace daga hannun dansanda a yankin Itu-Odukpani dake kan iyakar jihar Cross-River da Akwa-Ibom.   Matasane suka kwace Bindigar daga hannun wani dan sandan jihar Rivers dake cikin tawagar 'yansanda masu kula da tabbatar da dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi.   Matasan garin Odukpani dake jihar Cross-River sun harzuka da yanda suka ga jami'an 'yansanda na karbar cin hanci suna barin mutane daga jihar Akwa-Ibom dake da Coronavirus/COVID-19 na shigar Musu jiha. Grassroots reports sun ruwaito cewa 'yansandan na karbar daga Naira 500 zuwa 5000 dan barin fasinjoji shiga jihar Akwa-Ibom.   Hakanne yasa suka yi gangami da tunkarar 'yansanda har suka yi nasarar kwace bindigar daya. Daga baya. Mataimak...
Da Dumi-Dumi:Dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar lalata babban gurin da Boko Haram ke shirya hare-haren da take kaiwa

Da Dumi-Dumi:Dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar lalata babban gurin da Boko Haram ke shirya hare-haren da take kaiwa

Tsaro
Hedikwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa ta lalata wani guri da Tace nan ne Boko Haram ke shirya hare-haren da ta ke kai musu da farar hila wanda basu ji basu gani ba.   Hari  ya farune a Yuwe dake cikin dajin Sambisa da na jihar Borno kamar yanda sanarwar ta tabbatar. An dai samu Rahotannin cewa Boko haram na amfani da wajan kuma bincike ya tabbatar da hakan inda jirgin sojin sama da yayi shawagin leken Asiri ya ga tutar Boko Haram din.   Daga nanne fa sai aka tashi jirgin saman yaki da yayi luguden wuta akan maboyar inda ya lalata da kuma kashe wasu daga cikin 'yan kungiyar.   Kalli Bidiyon a kasa:   https://twitter.com/DefenceInfoNG/status/1273902734991863813?s=19 A baya dai mu  kawo muku yanda wani kwamishina a jihar Borno ya tabbata...
‘Yadda kawuna ɗan Boko Haram ya mayar da ni ganima’

‘Yadda kawuna ɗan Boko Haram ya mayar da ni ganima’

Tsaro
Yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 19 ga watan Yuni domin yaki da cin zarafin wadanda tashin hankali ya shafa a fadin duniya, a Najeriya wata baiwar Allah da muka boye sunanta ta shaida wa BBC cewa "'yan Boko Haram sun ci zarafin mu inda suka yi ta tarawa da mu."   Wannan matashiya dai ta shaida wa BBC irin yadda lamarin ya faru da ita lokacin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai hari a garinsu.   Ta ce " ranar wata Talata sai 'yan Boko Haram suka shigo garinmu suna kabbara inda suka karbe garin suka kuma kashe duk maza sannan sai suka kada duk mata zuwa daji bayan sun kone gari.   A ranar kawuna wanda kanen mahaifina ne ya zo ya ce na tashi na bi shi ni na zama ganima, inda ya tafi da ni kuma ya yi ta tara wa da ni."   Matashiyar ta ka...
‘Yan sanda a jihar Yobe sun cafke wani mutum da ake zargi da laifin fashi da makami tare da kama wasu mutum 2 da laifin yiwa yara kanana fyade 

‘Yan sanda a jihar Yobe sun cafke wani mutum da ake zargi da laifin fashi da makami tare da kama wasu mutum 2 da laifin yiwa yara kanana fyade 

Tsaro
Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Yobe ta ba da sanarwar cewa, 'yan sanda a jihar sun kama wani mutum da ake zargi da fashi da makami, mai suna Gambo Dahiru dake kauyen Bara Kakura. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar  Dungus Abdulkarim ya fitar ranar Alhamis. Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da yake kokarin karbar Naira miliyan uku daga hannun wanda abin ya shafa, mai suna Mamman Ahmed dake karamar hukumar Gulani. Haka zalika Ya ce, rundunar ta kara kaimi wajen gano sauran membobin kungiyar da suka tsere domin amsa tambayoyi tare kuma da fuskantar hukunci. Haka kuma rundunar ta bayyana cewa, a cikin wannan makon, 'yan sanda a garin Potiskum sun kama wani mutu...
Zanga-zangar Katsina: ‘Yan sanda sun saki Nastura Ashir

Zanga-zangar Katsina: ‘Yan sanda sun saki Nastura Ashir

Tsaro
Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya,Coalition of Northern Groups (CNG), ta tabbatar da sakin shugaban kwamitin amintattu na ƙunigyar wato Nastura Ashir Sharif bayan ya shafe kwanaki biyu a hannun 'yan sanda. A sanarwar da mai magana da yawun gamayyar kungiyoyin, Abdul-Azeez Suleiman ya sanya wa hannu, an saki Nastura ne sakamakon matsin lamba da ƙungiyarsu ta yi wa gwamnati tare da Ƙungiyar Dattawan Arewa da wasu kuma masu faɗa a ji na arewacin Najeriya da dai sauraren ƙungiyoyi. A hirarsa da BBC, Abdul-Azeez Suleiman, ya shaida wa BBC a ranar Laraba cewa an kama Ashir Sharif ne bayan sun kammala zanga-zanga a birnin Katsina inda suka yi kira a ɗauki mataki game da kashe-kashen da ke faruwa a yankin.
Da Dumi-Dumi:Yanzu haka ‘yan Bindiga na kai hari a kauyen Galadima na karamar hukukar Shiroro jihar Naija cikin darennan

Da Dumi-Dumi:Yanzu haka ‘yan Bindiga na kai hari a kauyen Galadima na karamar hukukar Shiroro jihar Naija cikin darennan

Tsaro
Labarin da muke samu da dumi-dumi daga jihar Naija na cewa, 'yan bindiga sun shiga garin galadina inda suke ta harbin kan mai uwa da wabi.   Majiyarmu wadda bata so a bayyana sunanta ba dake Garin Erena a karamar hukumar Shiroro na cewa mutane daga kauyen Galadima sai tururuwa suke cikin garin saboda harin dake waaka yanzu haka a cikin garin.   Harin 'yan bindiga dai na ci gaba da sanadin asarar dukigoyi da Rayuwa a Arewacin Najeriya abinda yake kara daukar hankalin manazarta wanda har hakan ya jawo zanga-zanga.