fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Tsaro

An sace mataimakin shugaban karamar hukumar Shelleng a jihar Adamawa

An sace mataimakin shugaban karamar hukumar Shelleng a jihar Adamawa

Tsaro
An sace mataimakin shugaban karamar hukumar Shelleng na jihar Adamawa, Kama Bakta. Wani jami’in karamar hukumar ya ce an sace Bakta ne a safiyar ranar Talata a garinsu, Bakta. “Abin bakin ciki, an sace mataimakin a yau misalin karfe 1:20 na 16 ga watan Yuni 2020 wannan bakar rana ce. Hon.Kama Lazarus BaktaMataimakin shugaban karamar hukumar shelleng, ”majiyar ta fada a cikin wani sako ga manema labarai. Wani mazaunin yankin ya ce, "masu satar sun shigo da yawansu dauke da bindigogi sannan suka shiga gidan dan siyasa da misalin karfe 2 na safe a ranar Talata." "Sun ta harbi cikin iska don shelanta isowarsu kuma nan da nan suka shiga suka dauke dan siyasan. "Duk abin ya kasance mai ban tsoro kamar yadda babu wanda ya iya samun karfin gwiwa don kalubalanci masu satar ...
An sace wata matar Aure a jihar Nasarawa

An sace wata matar Aure a jihar Nasarawa

Tsaro
Mahara a jihar Nasarawa sun sace matar shugaban matasan kabilar Eggon, Daniel Anyabuga. Lamarin ya farune a a daren jiya, Talata kamar yanda Rahotanni suka bayyana.   Maharan da suka kai 10 sun shiga gidan na shugaban Eggon da misalin karfe 10 zuwa 11 na dare inda suka dauki matar suka tafi da ita. Kwamishinan 'yansanda na jihar, Bola Longe ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace sun kama mutane 4 sannan kuma mashinan aka yi amfani dasu wajan harin suma an kamasu.   Ya kuma yi kira ga mutane da su bada hadin kai wajan samar da bayanan da zasu kai gakama wanda suka yi wannan danyen aiki.
Hukumar Soji ta kori janar dinnan da shekarar data gabata ya shiga Badakalar Miliyan 100

Hukumar Soji ta kori janar dinnan da shekarar data gabata ya shiga Badakalar Miliyan 100

Tsaro
Kotun Hukumar sojin Najeriya ta kori Majo Janar Hakeem Oladapo Otiki dake kula da rundunar sojin Sokoto daga aiki bayan ta sameshi da laifin almundahanar kudi.   Kotun tace za'a ragewa sojan Mukami daga Majo Janar zuwa Birgedia Janar inda za'a kuma koreshi aiki ta hanyar wulakanci da kaskanci. Saidai ai majalisar Koli ta sojin ta duba wannan hukunci dan tabbatar da shi ko kuwa akasin haka.   Hukuncin ya bukaci kudi Miliyan 135, da kudi dala 6,600, da kuma Miliyan 159 da aka kwato daga hannun janar din sojin duk a mayarwa da Hukumar Sojinsu.   Saidai Lauyansa, Bar. Israel Olorundare(SAN) ya bukaci a wa wanda yake wakilta sassauci.   Yace kamin yanzu Janar Otiki ya kasance hazikin soja da ya samu nasarori da dama a ayyukan da yawa hukumar so...
Mahara sun kashe mutum 105, sun kora 12,753 a Sokoto

Mahara sun kashe mutum 105, sun kora 12,753 a Sokoto

Tsaro
Jihar Sokoto ta rasa rayuka 105 sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da suka tilasta wa wasu 12,753 gudun hijira a Karamar Hukumar Birnin Magaji a cikin wata biyu.     Kananan yara 6,377‬ ne ke cikin ‘yan gudun hijira daga Birnin Magaji, inda ‘yan ta’adda suka kai hari a kauyuka goma, a cewar Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA).     Darekta Janar din SEMA Nasiru Aliyu ya ce mutum 60,000 ne ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira a jihar Sokoto.   Mutanen, a cewarsa sun yi kaura ne bayan ‘yan bindiga sun tayar da garuruwansu a jihar ta Sokoto da kuma jihohin Zamfara da Katsina da kuma Jamhuriyar Nihar.     “Gwamnati na kulawa da su tana ba su abinci da magunguna da sauran bukatu”, ya ce.
Kunyar jama’ar Katsina nake ji saboda na gaza kare rayukansu>>Gwamna Masari

Kunyar jama’ar Katsina nake ji saboda na gaza kare rayukansu>>Gwamna Masari

Tsaro
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana cewa kunyar mutanen jiharsa yake, baya iya kallonsu, saboda ya kasa cika alkawarin da ya dauka na kare rayukansu.   Gwamnan ya bayyana hakane a yayin ganawa da manema labarai kamar yanda The Cable ta ruwaito. Yace abinda 'yan bindigar ke yi koda dabbobi basa yinshi. Gwamnan yace yana iya bakin kokarinsa wajan baiwa jami'an tsaro hadin kai a yakin da suke da 'yan ta'addar.
An saki me tsaron lafiyar A’isha Buhari da yayi harbi a fadar shugaban kasa

An saki me tsaron lafiyar A’isha Buhari da yayi harbi a fadar shugaban kasa

Tsaro
Rahotanni sun bayyana cewa an saki Usman Shugaba, me tsaron lafiyar A'isha Buhari da yayi harbi a fadar shugaban kasa, Muhammadu Buhari lokacin hatsaniya tsakanin hadimin shugaban kasar,Tunde Buhari da iyalanshi.   Hutudole ya samo daga Sahara Reporters cewa an saki Shugaba ne a jiya, Litinin. Hakanan Rahotan ya kara da cewa Shugaba yasan abubuwa da yawa akan masu ruwa da tsaki a harkar gwamnati dake kallon A'isha Buhari a matsayin wata matsala dake hanasu cimma burinsu. Hakanan ya kara da cewa fadan bai kare ba dan kuwa A'isha Buhari ta cimma damarar daukar fansa kan wannan terere da aka mata a Duniya.
Kungiyoyin Arewa zasu fito Zanga-zangar nuna rashin jin dadin hare-haren ‘yan bindiga a yau

Kungiyoyin Arewa zasu fito Zanga-zangar nuna rashin jin dadin hare-haren ‘yan bindiga a yau

Tsaro
Gamayyar Kungiyoyin Arewa zasu gudanar da zan ga zanga domin nuna rashin jindadin su kan yadda matsalar tsaro ke cigaba da ta'azzara a yankin Aewacin Nijeriya.     Shugaban tafiyar Bashir Sharif ne ya bayyana hakan Jim kadan bayan kammala tattaunawar su a Abuja, in da yace za'a fara gudanar da zanga-zangar ne yau Talata 16+06-2020 kuma za'a fara fa Jihar Katsina duba sa yadda matsalar ke cigaba da barazana ga al'ummar jihar.   Lamarin ysaro ya ta'azzara a jihar Katsina wanda dama a baya an samu wasu matasa da suka fito yin zanga-zangar nuna rashin jin dadi amma ba a kungiyance ba a kauyen 'yan Tumaki.   Saidai wannan ne karon farko da wata kungiya zata fito a kungiyance ta yi zanga-zangar nuna rashin jin dadin matsalar tsaron kamar yanda Muka samo d...
Da Dumi-Dumi:’Yan Bindiga sun sace mutane 25 a daren jiya a Zamfara

Da Dumi-Dumi:’Yan Bindiga sun sace mutane 25 a daren jiya a Zamfara

Tsaro
Rahotannin dake fitowa daga jihar Zamfara na cewa 'yan bindiga da suka shiga garin Bindin na karamar hukumar Maru dake jihar Zamfara sun sace akalla mutane 25.   'Yan bindigar sun tare hanyar shiga garin inda suka rika shuga gida-gida suna zakulo mutane. Bayan sun gama tarasu suka shiga daji dasu suka kuma bukaci 'yan uwansu da su biya kudin fansa kamin a sakesu.   Wani mutum daya ya kubuta daga hannunsu yayin da suka saki wata mata saboda tana shayar da jaririnta.   Ba'a samu jin ta bakin kakakin 'yan bindigar jihar,Muhammad Shehu ba a yayin hada wannan rahoto kamar yanda Daily Trust ta ruwaito.
El-Rufa’i ya janye jami’an tsaro a kan iyakokin Kaduna

El-Rufa’i ya janye jami’an tsaro a kan iyakokin Kaduna

Tsaro
Gwamnatin Kaduna ta bayar da umurnin janye dukkanin shingayen da aka datse kofofin shiga jihar tare da ba jami'an tsaro umurnin su janye. Sanarwar da aka wallafa a shafin Twitter na gwamnatin jihar ta ce za a toshe hanyoyin ne kawai lokacin da dokar hana fitar dare ta fara aiki daga karshe 8 na dare zuwa 5 na safe. Sannan gwamnati ba za ta sake tura jami'ai ba a kan iyakokin jihar.
Jami’an ‘yansanda sun saka ladar Miliyan 5 kan shugaban ‘yan ta’addar Katsina

Jami’an ‘yansanda sun saka ladar Miliyan 5 kan shugaban ‘yan ta’addar Katsina

Tsaro
Jami'an 'yansanda sun bayyana cewa suna neman Adamu Aliero Yankuzo dan kimanin shekaru 45 wanda shine shugaban 'yan ta'addar dake aika-aika a tsakanin Zamfara da Katsina.   Kaamishinan 'yansandan jihar Katsina, Sanusi Buba ne ya bayyana haka a ganawar da yayi da manema labarai. Yace duk wanda ya kawo musu Adamu wanda dan Asalun Tsafene a rai ko a mace akwai ladar Miliyan 5.