fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Tsaro

Sojoji sunyi Nasarar kashe wasu Mahara tare da kwato makamai a jihar Benue

Sojoji sunyi Nasarar kashe wasu Mahara tare da kwato makamai a jihar Benue

Tsaro
An kashe wasu Mahara biyu da ake zargi Makiyaya ne a daran ranara juma'a a  wata musayar wuta da sojojin hadin gwiwa na rundunar soji mai suna OPWS tai a jihar Benue, bayan da rundunar ta samu rahoton 'yan bindigar sun mamaye yankin Tse Chembe da ke karamar Hukumar Logo na jihar Benue. Wannan ya zo ne a daidai lokacin da gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta ayyana makiyayan da ke kisa a Benue da sauran sassan kasar a matsayin kungiyar 'yan ta'adda. Jaridar Vanguard ta rawaito cewa maharan  suna daga cikin wadanda a baya suka afkawa al'ummomin yankin a ranar juma’a da daddare inda suka kashe mazauna garin har mutane biyu tare da raunata wasu biyu. A cewar wata majiya a yankin, maharan sun kai hari kan mazauna yankin ne da misalin karfe 6:45 na yamma,...
Yawan mutanen da ake kashewa yanzu sun fi wanda aka kashe a yakin Basasa>>Edwin Clark

Yawan mutanen da ake kashewa yanzu sun fi wanda aka kashe a yakin Basasa>>Edwin Clark

Tsaro
Dan siyasa kuma tsohon Ministan Labarai daga kudancin Najeriya, Edwin Clark ya bayyana cewa yawan mutanen da ake kashewa a Najeriya a yanzu ya fi wanda aka kashe a lokacin yakin Basasa.   Ya bayyana hakane a ganawar da aka yi dashi da Sunnews.  Yace babu Dimokradiyya a Najeriya domin mulkin da ake yi a yanzu yama fi na Soja Muni. Ya kara da cewa dan hakane ma suka kai gwamnati kara inda suke neman a biyasu Biliyan 50 a matsayin diyyar na daidai ba da aka aikata musu.   Da yake magana akan matsalar tsaro yace abubuwa kullun sai kara tabarbarewa suke, uace yawan mutanen da ake kashewa a Najeriya a yanzu yafi wanda aka kashe a lokacin yakin basasa.   Yace ka duba kasar Amurka, mutum 1 ne aka kashe amma gaba daya hankula sun tashi amma a Najeriya sai a k...
Sojojin da suka Ajiye aiki lokacin Ritayarsu ne yayi bawai gazawa bace>>Hukumar Sojin Najeriya

Sojojin da suka Ajiye aiki lokacin Ritayarsu ne yayi bawai gazawa bace>>Hukumar Sojin Najeriya

Tsaro
Hukumar Sojin Najeriya ta karyata cewa gazawace tasa sojoji 386 suka ajiye aikin sojan inda tace wanda suka fitar da wancan labari masu goyon bayan kungiyar Boko Haram ne dake son kashewa sojojin Najeriya karfin gwiwa.   Hukumar tace sojojin sun kammala aikin su ne na soja kuma lokacin Ritayarsu yayi shine suka ajiye aiki. Ta kara da cewa bata cikin rashin sojojin da zasu yi yaki domin kwanannan 'yan Najeriya masu kishin kasa 4,600 suka shiga aikin soja kuma da yawa daga cikinsu sun amince a sakasu cikin dakaru na musamman da zasu yaki ta'addanci.
‘Yan bindiga sun kai hari a wasu kauyuka dake Kudancin Kaduna Inda suka kashe mutane 20

‘Yan bindiga sun kai hari a wasu kauyuka dake Kudancin Kaduna Inda suka kashe mutane 20

Tsaro
'Yan bindiga a ranar Juma’a, sun kai hari kan al’ummomin Chibuak da Kigudu, a karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna, inda suka kashe mutane kimanin 20 yayin da wasu al'ummomi dake kauyukan su kai batan dabo. Haka zalika A ranar Asabar, an sake kai wani hari a Kigudu II inda mazauna kauyen ke shirin binne gawarwakin wasu daga cikin wadanda abin ya shafa wadanda sun kasance mabiya darikar Katolika ne. Rahotanni sun bayyana cewa a kalla mutane 20 ne suka rasa rayukan su, bayan da aka ka she mutane a kalla 9 a kauyan Chibuak inda kuma 'yan bindigar suka kashe mutane 11 a kauyan Kigudu., “An dai kai harin ne a ranakun Alhamis da Juma'a da tsakar dare. A cewar Mazaunan kauyan sun bayyana cewa sun shirya binne ga warwakin wadanda lamarin ya shafa a Kigudu da safiyar ranar Asabar, amma...
Mahara sun kashe mutane 20 a kauyukan Kaduna

Mahara sun kashe mutane 20 a kauyukan Kaduna

Tsaro
Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa mahara a dararen Alhamis da Juma'a sun afkawa kauyukan Chibuak Kigudu na karamar hukumar Kauru inda suka kashe mutane 20.   A ranar Asabar ma an sake samun wani harin yayin da mutane suka taru zasu yi jana'izar wanda aka kashe, saidai jami'an tsaro sun hana maharan cimma burinsu inda suka korasu. Me magana da yawun rundunar 'yansandan jihar, ASP Muhammad Jalige yace idan ya samu bayani akan harin zai tuntubi 'yan Jarida.   Saidai Wani Fasto, Aron Tanko ya tabbatarwa da Manema labarai cewa mutanen da aka kashe sun kai 20 kuma da dama sun bace, ba'a gansu ba bayan harin.   Yace mutane 9 ne aka kashe a kauyen Chibuak sai kuma 11 a kauyen Kigudu. Yayi zargin cewa fulani makiyayane da miyagun bindigu ke kai musu hare-ha...
Gwamnan Jihar Benue Ya Bukaci Gwamnatin Tarayya Data Ayyana Fulani Makiyaya A Matsayin ‘Yan ta’adda

Gwamnan Jihar Benue Ya Bukaci Gwamnatin Tarayya Data Ayyana Fulani Makiyaya A Matsayin ‘Yan ta’adda

Tsaro
Gwamnan jihar Binuwai Samuel Ortom ya bukaci Gwamantin Tarayya ta ayyana makiyaya dauke da makami masu karkashe mutane a kauyukan jiharsa a matasyin ‘yan ta’adda. Ortom ya ce kiran ya zama wajibi saboda yawaitar hare-harensu na ba gaira ba dalii a sassan jihar a ‘yan watannin nan, domin doka ta hukunta su. Sanarwar da kakakin gwamnan, Terva Akase ya fitar ta ce ko a ranar Juma’a, ‘yan bindigar sun kashe mutum bakwai tare da jikkata wasu da dama a kauyen Tse-Chembe na Karamar Hukumar Logo ta jihar. Terva Akase wanda ya jaddada dokar jihar ta haramta yawo da dabbobi ya yi tir da hare-haren tare da cewa babu wanda zai saba dokar ya kuma rika zubar da jinin mutane sai ‘yan ta’adda. Ortom wanda ya yaba wa sojojin rundunar Operation Whirl Stroke bisa daukinda suka kai wa jama’a...
Yan Bindiga Sun Sace Jami’in Gwamnati Da Wasu Mutane Biyu A Jihar Ekiti

Yan Bindiga Sun Sace Jami’in Gwamnati Da Wasu Mutane Biyu A Jihar Ekiti

Tsaro
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sun kai hari a safiyar ranar Juma’ar da ta gabata a garin Isinbode Ekiti a karamar hukumar Ekiti ta gabas da ke jihar Ekiti, sannan suka yi garkuwa da mutane uku. Majiyoyin sun ce maharan, wadanda suka kai kimanin 10 sun kai hari a kan wata ma'aikata da ke kusa da Isinbode - laying Ode kuma suka kwace wa ma'aikatan kamfanin abubuwan su kafin su sace mutane biyu a wurin. Daya daga cikin majiyar ya ce 'yan bindigar bayan sun bar gurin sun kuma afkawa wani wata motar Hilux a gefen hanya dauke da bindigogi sannan kuma suka sace daya daga cikin mazaunin motar da aka yi imanin cewa wani jami'in gwamnati ne. “Harbin direban motar Hilux din ya tilasta shi tsayawa a kan babban titin, yayin da suka sace mutum guda da aka yarda cewa bab...
Shugaba Buhari Yayi Kira Don Hadin Gwiwa Tsakanin Kasashen ECOWAS Don Fuskantar Matsalolin Tsoro

Shugaba Buhari Yayi Kira Don Hadin Gwiwa Tsakanin Kasashen ECOWAS Don Fuskantar Matsalolin Tsoro

Tsaro
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira da a kara hadin gwiwa tsakanin kasashen kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) domin yakar ta'addanci a yankin. Shugaba Buhari ya yi wannan kiran ne a ranar Asabar a yayin bikin yaye manyan jami’ai 181 a Kwalejin Sojoji dake Jaji a Jihar Kaduna. Shugaban ya kuma kara da cewa, Najeriya, tare da hadin gwiwar kawayenta, ba za su zauna ba har sai 'yan ta'addar Boko Haram a yankin tafkin Chadi da sauran gungun' yan ta'adda da ke yin ta'addanci a yankin Afirka ta Yamma sun kare. Da yake Magana ta bakin Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya), Shugaba Buhari ya yaba wa Sojojin Kasar saboda ci gaba da daukar matakan da suka dace kan kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta. Tare da shi gwamnan ji...
Dakarun sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga 2 a Taraba

Dakarun sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga 2 a Taraba

Tsaro
Sojojin Najeriya sun kashe 'yan Bindiga 2 a jihar Taraba. Hedikwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa sojojin na Rundunar Operation Whirl Stroke sun samu bayananan sirri kan Harin da 'yan Bindigar suka kai kauyen Logo dake jihar Benue. Yace an tashi sojoji dan tunkarar wadannan mahara amma kamin su je sun gudu bayan kashe mutane 2 a kauyen. https://twitter.com/DefenceInfoNG/status/1281912868737294338?s=19 Sojojin sun bi sahun Barayin inda suka iskesu a Arufu, jijar Taraba suka kuma kashe 2 daga ciki, wasu suka gudu da raunuka.
Sojoji 356 na son barin aiki saboda gajiya da Aikin

Sojoji 356 na son barin aiki saboda gajiya da Aikin

Tsaro
Rahota ni daga gidan Sojan Najeriya na cewa sojoji 356 na son barin aikin saboda gajiya da aikin wanda hakan na nuni da rashin karfafa gwiwa daga shuwagabannin sojin, kamar yands hutudole ya samo daga Premium times.   Majiyar tamu ta bayyana cewa ta samu daga wata majiya daga gidan sojan cewa Sojoji 356 ne keson barin aiki saboda gajiya da aikin sannan kuma akwai 24 dake saon barin aikin saboda karbar sarautun gargajiya. Tuni dai shugaban sojin, Janar Tukur Yusuf Buratai ya amince da barin aikin sojojin.   Majiyar tace akwai kuma wasu sojoji  da suka wugar da bindigunsu da kakinsu suka tsere saboda gajiya da aikin.   Saidai me magana da yawun hukumar Sojin Majo Sagir Musa yace wannan labari ba gaskiya bane, yace akwai karfin gwiwa sosai tare da sojoj...