
An dakile damfarar Siyen Abin rufe hanci na Daruruwan Miliyoyin Naira
'Yan sanda dake binciken aikata ba daidai ba na kasa da kasa da ake kira da Interpol sun bayyana cewa sun dakile wata damfarar Yuro Miliyan 1.5, kwatankwacin sama da Naira Miliyan 600.
Yanda Lamarin ya faru shine an samu wani me sayen abin rufe hanci wanda shi kuma wani da yayi amfani da Email din karya wanda yayi amfani da sunan wani kamfani mallakar kasar Sifaniya da kuma shafin Yanar Gizo na karya yace yana dashi.
Me sayarwar da farko yace yana da abin rufe fuskar daya kai guda Miliyan 10 amma daga baya ya mika me sayen zuwa wajan wani Kamfani na kasar Ireland wanda shi kuma daga baya ya mikashi wajan wani me sayewa na kasar Netherlands.
Daga karshe dai me sayen ya aika kudi Yuro Miliyan 1.5 da sunan za'a fara sayar masa da abin fuska na guda Miliy...