fbpx
Saturday, August 13
Shadow

Tsaro

Boko Haram Sun Kaiwa Tawagar Tsohon Gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff Mummunan Hari

Boko Haram Sun Kaiwa Tawagar Tsohon Gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff Mummunan Hari

Tsaro
INNALILLAHI WA INNAA ILAIHI RAJI'UN Dazun nan Boko Haram suka kaddamar da mummunan harin ta'addanci akan tawagar tsohon gwamnan jihar Borno Sanata Ali Modu Sheriff lokacin da suke rakiyar tawagar tsohon gwamnan daga Abuja zuwa garin Maiduguri don yin jana'izar mahaifinsa da ya rasu, sai Boko Haram suka kaddamar musu da mummunan hari a daidai garin Auno dake kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.     'Yan ta'addan sun hallaka wasu jami'an 'yan sanda masu bada kariya na musamman Special Protection Unit (SPU) rundina ta 12 kuma harin ya rutsa da fararen hula, gawarwakinsu yana asibitin kwararru na garin Maiduguri.     Wadanda suka samu shahada Insha Allah a wannan mummunan hari sune Cpl Mustapha Yunusa, Cpl Abubakar Idris, sannan 'yan ta'addan sun taf...
An kama ‘yansandan da suka yi fada a tsakiyar Titi

An kama ‘yansandan da suka yi fada a tsakiyar Titi

Tsaro
A jiyane wani bidiyon 'yansandan 2 ya watsu sosai a shafukan sada zumunta inda aka gansu suna fada da juna.   Wasu rahotannin dai da basu tabbata sun bayyana cewa suna fadanne akan Rabon cin Hanci.   'Yansandan wanda hukumar ta shafinta na yanar gizo ta bayyanasu da sunayen Ozimende Aidonojie ta bayyana cewa suna can ana tuhumarsu kuma za'a musu hukunci daidai da dokar hukumar.   Ta kara da cewa za'a bayyana irin hukuncin da aka dauka akansu bayan an kammala bincike.      
An kashe ‘yansanda 2 a Kamfanin Atiku

An kashe ‘yansanda 2 a Kamfanin Atiku

Tsaro
Wasu 'yan bindiga sun kashe 'yansanda 2 a jihar Adamawa.   'Yansandan ASP Yohanna da DSP Gbenga an kashesune a RicoGado, kamfanin yin abincin Dabbobi na tsohon shugaban kasa, Atiku Abubakar dake jihar.   Rahoton Punch yace wani jami'an tsaro ya shaidawa jaridar cewa yana zargin kamar dama an shirya kashe 'yansandanne inda aka jasu zuwa inda abin ya faru.   Me magana da yawun hukumar yansandan jihar, DSP Sulaiman Sulaiman Nguroje ya bayyana cewa tabbas lamarin ya faru amma suna bincike akai.
Daya daga cikin masu tsaron Shugaban kasa Buhari ya mutu

Daya daga cikin masu tsaron Shugaban kasa Buhari ya mutu

Tsaro
Shugaban kasa Buhari ya rasa daya daga cikin masu tsaron sa Lawal Mato kwanaki uku bayan jana'izar Shugaban Ma'aikatan Shugaba Muhammadu Buhari, Mallam Abba Kyari, Shugaban kasar ya sake rasa daya daga cikin masu tsaron lafiyar sa, Babban Jami'in sa mai suna Lawan Mato. Sanarwar mutuwar tasa tazo ne ta bakin Babban Mataimaki na Musamman ga shugaban kasa a kan kafofin yada labarai Mallam Garba Shehu a Abuja ranar Talata. Shehu a cikin sanarwar ya ce marigayin ya sha fama da jinya har tsawan shekaru uku a sakamakon fama da yai da ciwan sikari'diabetes'. Shugaba Buhari ya bayyana jami'in a matsayin jajir tacce.Wanda yayi aiki da shi tun kafun yayi nasarar cin zabe a shekar dubu biyu da 15. A karshe Shugaba Buhari yayi jajan rashin jami'in tare da yi masa addu'a.
‘Yan Boko Haram na rige-rigen mika wuya, shekau ma zai mika wuya kwanannan, An kashe Boko Haram 13>>Hukumar Soji

‘Yan Boko Haram na rige-rigen mika wuya, shekau ma zai mika wuya kwanannan, An kashe Boko Haram 13>>Hukumar Soji

Tsaro
Rundunar sojin Najeriya ta dakile harin da mayakan Boko Haram Suka yi yunkurin kaiwa a garin Gaidam na jihar Yobe a jiya,Litinin.   Rahotanni sun bayyana cewa,Boko Haram din basu ji dadadi ba a hannun sojojin na rundunar Operation Lafiya Dole inda suka hanasu cimma burinsu na kaddamar da hari a Geidam.   Rahotan yace an kashe 'yan Boko Haram din su 13, sannan an kwato bindigogi  AK47 guda 6 da motocin yaki 2.   Babu dai soja ko daya da aka kashe a harin.   Hakanan hukumar sojin ta bayyana cewa, nan gaba kadan shugaban kungiyar ta Boko Haram, Abubakar Shekau zai mika wuya saboda bashi da gurin Buya.   Hakanan me magana da yawun hukumar tsaron,Majo Janar John Enenche ya bayyana cewa akwai mayakan Boko haram din da dama dake mika wuya. ...
Mun kashe ‘yan Boko Haram sama da 100-Sojin Najeriya

Mun kashe ‘yan Boko Haram sama da 100-Sojin Najeriya

Tsaro
Rundunar Sojin Najeriya ta yi shelar kashe mayakan Boko Haram 105 a samamen da dakarunta suka kaddamar kan maboyar 'yan ta'addar da ke Bunu-Gari a Jihar Yobe.     Daraktan Yada Labaran Rundunar, Kanar Sagir Musa ya sanar da haka a daidai lokacin da shugaban sojin Janar Yusuf Tukur Buratai ya tare a arewa maso gabashin kasar  domin ganin an murkushe mayakan kungiyar baki daya.     Kanar Musa ya ce, runduna ta biyu ta dakarun da ke yaki da kungiyar Boko Haram a karkashin Birgediya Janar Lawrence Araba, ta samu nasarar kashe mayakan sakamakon bayanan sirri da aka tsegunta musu.     Daraktan Yada Labaran ya ce, shugaban rundunar sojin Janar Buratai ya bayyana farin cikinsa da wannan gagarumar nasara lokacin da ya ziyarci dakarun domin ga...
Maharan da suka kashe mutum 47 a Katsina za su yaba wa aya zaki>>Buhari

Maharan da suka kashe mutum 47 a Katsina za su yaba wa aya zaki>>Buhari

Tsaro
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi tir da harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a yankin Kananan Hukumomi Uku na jihar Katsina inda akalla mutane 47 suka rasa rayukan su.     Akalla mutum 47 ne mahara suka kashe a harin da suka kai kananan hukumomin Dutsinma, Danmusa da Safana, jihar Katsina.     Kakakin ‘yan sandan jihar Gambo Isah, ya tabbatar da aukuwar harin, inda ya ce tuni an aika da jami’an tsaro yankunan domin samar da zaman lafiya.     Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a takarda da kakakin fasar shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, yanar Lahadi ya na mai cewa hakan ya yi matukar tada masa hankali da bacin rai sannan ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da kada su karaya a dalikin aukuwar irin wannan abu cewa gwamnati za ta ci gab...
‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 83 A Katsina Har Lahira

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 83 A Katsina Har Lahira

Tsaro
'Yan Bindiga dauke da manyan makamai sun kai tagawayen hare-hare a wasu kauyukan kananan hukumomin Dutsinma da Safana da kuma Danmusa da ke jihar Katsina inda suka kashe mutane sama da tamanin da ukku. Da yawa kuma sun baro kauyukan su sun kwararo zuwa helkwatar karamar hukumar Safana da Danmusa da kuma Dutsinma, domin yin gudun hijira.     Tagawayen hare-haren yan bindigar ya faru a safiyar jiya asabar tun daga karfe takwas na safiya, har zuwa karfe daya da rabin yammacin jiya.     Wani mazaunin daya daga cikin garuruwan ya shaidawa RARIYA ta waya cewa yan bindigar, sun zo ne da rana ido na ganin ido, bisa babura sama da dari ukku, kuma kowane da goyan mutum daya zuwa biyu dauke da bindigogi, su ka yi ta harbi ba kaukautawa a duk garin da suka dira. ...