
Gwamnatin tarayya zata dauki ma’aikata miliyan 1 su yi aikin kidaya
Hukumar kula da Kidaya ta kasa, NPC ta bayyana cewa, zata dauki mutane miliyan 1 dan su gudanar da aikin kidaya.
Shugaban hukumar a jihar Ekiti, Deji Ajayi ne ya bayyana haka inda yace za'a yi amfani da fasahar zamani wajan gudanar da kidayar.
Yace kuma za'a yi kokarin ganin an yi amfani da gaskiya wajan aikin dan kada masu kumbar susa su yi kaka gida akai.