fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Uncategorized

“Ba’a yabon dan kuturu sai ya shekara da yatsu”: Anyi cece kuce akan wannan hoton na Hadiza Gabon da dan uwanta

“Ba’a yabon dan kuturu sai ya shekara da yatsu”: Anyi cece kuce akan wannan hoton na Hadiza Gabon da dan uwanta

Uncategorized
Wannn hoton na jarumar fim din hausa, Hadiza Gabon da wani danuwanta data saka a shafinta na sada zumunta da muhawara ya jawo ce-ce-kuce sosai, A yayinda rubutun datayi a jikin hoton ya nuna cewa wannan dan uwantane na jini, wasu daga cikin mabiyanta sun nuna cewa hoton ya burgesu, wasu kuma suka fadi cewa gaskiya koda dan uwantane addinin musulunci lamunci su rika irin wannan kusansanceniyar da itaba. Misali: daya daga cikin wadanda suka bayyana ra'ayoyin nasu yace " Ba'a yabon dan kuturu saiya shekara da yatsu, meyasa 'yan fim kukewa diokar Allah karan tsaye? Ke da muke ganin kinada mutunci, Ke kuma Hadiza yanzu wanan abu da kikayi menene marabarki da Rahama Sadau?" Karin hotunan ra'ayoyin mutane akan wannan hoton.
Ya cigaba da nuna mata soyayya duk da wuta ta canja mata kamanni

Ya cigaba da nuna mata soyayya duk da wuta ta canja mata kamanni

Uncategorized
Wadannan masoya labarin su yana da taba zuciya, Namijin sunanshi Micheal ita kuma macen sunanta Turia, sun fara soyayya tun a makaranta, koda yake shi Micheal ne ya nunamata soyayya lokacin amma ita tana kallonshine a matsayin abokin data shaku dashi kawai amma ba soyayyaba. Sun kammala makaranta Micheal ya zama dan sanda ita kuma ta zama injiyar hakar ma'adanai, a lokacin soyayyarsu ta fara yin karfi, Turia ta amince dashi a matsayin saurayinta. Wata rana da dukansu bazasu taba mantawa da itaba gobara ta kama gida a lokacin Turia na ciki kuma ta kasa samun hanyar fita, Allah ya kaddara bata mutuba amma ta kone halittarta gaba daya ta canja. Haka Micheal yazo ya rika zama da ita a asibiti lokacin bata san inda kanta yakeba, baya zuwa ko'ina, a karshema ya ajiye aikinshi saboda ya sam...
Anyi bikin nuna kwalliyar akarnuka a Ingila

Anyi bikin nuna kwalliyar akarnuka a Ingila

Uncategorized
A jiya Lahadine akayi wani taron masu sha'awar karnukan pug a kasar Ingila, karnukan dai ba irin wadanda muke dasu bane anan, zaka gansu da tattararrar fuska da kuma gajeren hanci da idanu ciki-ciki amma manya. Haka kuma kananan karnukanne ake zuwa dasu irin wannnn biki banda manya. Taron anayinshine kamar biki yanda masu irin wadannan karnukan zasu yi musu kwalliya daban-daban su fito dasu zuwa gurin taron. An shirya wasannin debe kewa kala-kala a gurin taron da kuma sayar da kayan ciye-ciye da tande-tande. Wani mutum me suna Martin ne ya shirya wannan bikin saboda tunawa da wani karen danshi daya taba bacewa aka ganoshi amma ya mutu kuma masu irin wadannan karnuka sun bayar da hadin kai inda sukayita zuwa dasu suna zagayawa a gurin.

An hanani aure saboda zargin Luwadi>>Adam A. Zango

Uncategorized
Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Adam A. Zango, ya ce babban burinsa shi ne ya kware wajen magana da harshen Turanci. Zango, wanda aka haifa a garin Zangon Kataf na jihar Kaduna, ya yi karatun sakandare a birnin Jos na jihar Plateau ne. Jarumin ya ce zai bar sana'arsa nan da dan wani lokaci domin ya je ya ci gaba da karatun boko. A yanzu haka dai jarumin ya dauki malamin da yake ba shi darussa a gida, kafin ya koma makaranta don ci gaba da karatun. "Yanzu haka na kammala sakandare kuma ina son ci gaba da karatu, ko da zuwa matakin difiloma ne. Abin da nake so shi ne na iya Turanci sosai," in ji Adam Zango a wata hira da ya yi da BBC. Sai dai wani abu da Adam ya ce yana ci masa tuwo a kwarya shi ne yadda wasu 'yan boko suke masa kallon jahili duk kuwa da cewa "na yi karatun bo...
Gwamnan Kaduna, M. Nasiru El-Rufai tare da yaranshi a cikin jirgin kasa

Gwamnan Kaduna, M. Nasiru El-Rufai tare da yaranshi a cikin jirgin kasa

Uncategorized
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai kenan tare da yaranshi a cikin jirgin kasar dake zurga-zirga tsakanin Abuja da Kaduna, hotunan Gwamnan sun kayatar da mutane kuma ganin manyan mutane na amfani da jirgin kasar Kaduna zuwa Abuja, mutane da dama musamman wadanda basu taba yin tafiya cikin jirgin kasaba, suna sha'awar bin wannan jirgi domin suma suji yanda yake. Karin hotuna.

Kedai ki dogara da Allah

Uncategorized
Wasu matan sun samu mafi munin mutum, me sabon Allah(bama yiwa kowa fatan haka) a matsayin miji, kamar yanda Asiya ta auri fir'auna, amma hakan baisa ta canja kyawawan dabi'untaba da biyayya ga dokokin Allah ba. Wasu kuma sun samu mafi kyawun halin mutane da biyayya ga Allah, kamar Annabawan Allah, amma duk da haka sun hallaka, misali matar Annabi Lut(A.S). Wasu matan kuma basu samu yin aure ba kwatakwata a ruyuwarsu, kamar mahaifiyar Annabi Isa(A.S) wato Maryam(A.S) Amma kuma Allah ya daukakata fiye da kowace mace a Duniya. Kedai ki dogara ga Allah ki kuma nemi taimakonshi a koda yaushe, Allah yasa mu dace. Amin.
“Nagode da addu’ar da masoyana sukamin”>>Jamila Nagudu

“Nagode da addu’ar da masoyana sukamin”>>Jamila Nagudu

Uncategorized
Jarumar fim din hausa, Jamila Umar, Nagudu ta mika godiya ga wadanda sukaje dubata a asibiti da kuma masoyanta da suka mata addu'ar samun lafiya. Ga sakon data fitar kamar haka. "Allah mungode maka Allah kakaramana lafiya Allah marasa lafiya na gida da asibiti birni da kauye Allah kabasu lafiya akarshe yan uwa masoyana da abokan arziki dasukazo dubani asibiti dama wadanda basu samu damaba suke gida suka tayani da addu'a ina godiya nagode sosai Allah yabar zumunci"