fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Labarin Real Madrid na yau

Magoya bayan Real Madrid sun fara sarewa akan wasan su da Manchester City ganin yadda Girona ta lallasa su daci 4-2

Magoya bayan Real Madrid sun fara sarewa akan wasan su da Manchester City ganin yadda Girona ta lallasa su daci 4-2

Labarin Real Madrid na yau, Wasanni
Magoya bayan Real Madrid sun fara sarewa akan wasan su da Manchester City ganin yadda Girona ta lallasa su daci 4-2. Real Madrid tasha kashi daren jiya daci hudu da biyu a hannun kungiyar Girona a gasar La Liga. Yayin da zakakurin dan wasan Girona Castellanos yaci gabadaya kwallayen guda hudu. Sai ita kuma Madrid Vinicius da Vazquez suka cu mata biyu.
Real za ta karbi bakuncin Valladolid a La Liga ranar Lahadi

Real za ta karbi bakuncin Valladolid a La Liga ranar Lahadi

Labarin Real Madrid na yau, Wasanni
Real Madrid za ta fafata da Real Valladolid a wasan mako na 27 a gasar La Liga ranar Lahadi a Santiago Bernabeu. Real wadda take ta biyu a teburin La liga mai maki 56 tana da tazarar maki 15 tsakaninta da Barcelona ta daya mai maki 71. Ranar 30 ga watan Disambar 2022, Real ta je ta ci Valladolid 2-0 a La Liga, Karim Benzema ya fara ci mata kwallo a bugun fenariti a minti na 83, sai ya kara na biyu a minti 89. Wasan farko da Real za ta buga tun bayan da aka kammala karawar kasa da kasa da Fifa kan ware don buga manyan wasannin tawagogin duniya.
Real za ta rage tazarar maki 11 tsakaninta da Barcelona zuwa takwas, idan ta ci Elche ranar Laraba

Real za ta rage tazarar maki 11 tsakaninta da Barcelona zuwa takwas, idan ta ci Elche ranar Laraba

Labarin Real Madrid na yau
'Yan wasan Real da za su kara da Elche a La Liga   Real Madrid za ta karbi bakuncin Elche a wasan mako na 21 a La Liga da za su kara a Santiago Bernabeu ranar Laraba. Ranar 19 ga watan Oktoban 2022, Real ta je ta ci Elche 3-0 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya. Real Madrid tana ta biyu a teburi La Liga da tazarar maki 11 tsakaninta da Barcelona mai jan ragama mai maki 56. Elche wadda take da maki tara tana ta karshen teburin La Liga ta 20 kenan. Ranar Asabar Real ta lashe World Club Cup, bayan cin Al Hilal 5-3 a Morocco. Tuni Carlo Ancelotti ya bayyana 'yan wasan da zai fuskanci Elche 'Yan wasan Real Madrid: Masu tsaron raga: Lunin, Luis López da kuma Cañizares. Masu tsaron baya: Carvajal, Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Odri...
Ku yi min hakuri, nasan ban tabuka abin azo a gani ba>>Eden Hazard ya baiwa magoya bayan Real Madrid hakuri

Ku yi min hakuri, nasan ban tabuka abin azo a gani ba>>Eden Hazard ya baiwa magoya bayan Real Madrid hakuri

Labarin Real Madrid na yau, Wasanni
Tauraron dan wasan Real Madrid,  Eden Hazard ya bayyana cewa yana baiwa magoya bayan kungiyar Real Madrid hakuri kan rashin tabuka abin azo a gani tun bayan komawa kungiyar daga Chelsea.   A shekarar 2019 ne dai Hazard ya koma Real Madrid daga Chelsea akan Yuro Miliyan 100, saidai rauni ya hanashi yin aiki yanda ya kamata.   Saidai a wannan kakar duk da yake yana nan qalau, sau 3 kawai ya bugawa kungiyarsa ta Real Madrid wasa.   Hazard yace shekara daya ta rage masa a Real Madrid kuma yana son ya nunawa masoyansa gwanintarsa amma yana bayar da hakuri.
Carlo Ancelotti ya zarta tarihin Sir Alex Fergusson bayan Madrid ta lallasa Celtic da ci 5-1

Carlo Ancelotti ya zarta tarihin Sir Alex Fergusson bayan Madrid ta lallasa Celtic da ci 5-1

Labarin Real Madrid na yau
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta lallasa Celtic da ci 5-1 a wasan da suka buga na Champions league da yammacin yau.   Luka Modric, Rodrigo, Marco Asensio, Vicious, da Valverde ne suka ciwa Real Madrid kwallayen.   Yayin da a bangaren Celtic, Jota ne ya ci musu kwallo.   Da wannan nasara, Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti ya zarta Sir Alex Fergusson a yawan nasara a gasar Champions league inda yake da 103, yayin da Sir Alex Fergusson ke da 102.   Duk da cin da aka musu, magoya bayan Celtic sun rika musu tafi bayan da aka kammala wasan, inda 'yan wasan suma suka jinjinawa masoyan nasu.   Da wannan nasara, Real Madrid ta dare saman group F.