fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Wasanni

Hukumomin kwallan kafar turai a yau zata gudanar da wani taro

Hukumomin kwallan kafar turai a yau zata gudanar da wani taro

Wasanni
An dakatar da gaba daya manyan gasannin lig na kwallon kafa a kasashen nahiyar Turai a makon da ya gabata, a wani al’amari da ya jefa wasan kwallon kafa a cikin wani kalubalen da bai taba fuskanta ba a wannan zamani, kuma bisa ga dukkan alamu, dole ne ma a dau mataki a kan gasannin zakarun nahiyar Turai, wato Champions League da Europa League. Hukumar kwallon kafar Turai a yau Talata za ta gudanar da wani taro na wakilai 55 na hukumomin kwallon kafa na kasashe da kungiyoyi, sannan daga bisani ta gudanar da taron majalisar zartaswarta a shelkwatarta da ke Switzerland. Nahiyar Turai ta kasance tamkar cibiyar wannan annoba ta coronavirus, inda yanzu haka hukumomi suka garkame kofofi a Italiya da Spain, yayin da Faransa ke biye, haka kuma sauran kasashe a nahiyar suke garkame iyakoki do...
Pogba ya kafa gidauniyar yaki da Coronavirus

Pogba ya kafa gidauniyar yaki da Coronavirus

Wasanni
Shahararren dan wasan Manchester United Paul Pogba ya kafa wata gidauniya don tara kudin yaki da cutar coronavirus.   Wannan cuta dai ta karade duniya, inda yanzu haka ta harbi mutane 167,000, tare da kashe dubu 6 da dari 5.   Annobar dai ta shafi harkar wasannin motsa jiki musamman kwallon kafa, inda a nahiyar Turai aka dakatar da dukkannin gasannin kwallon kafa, haka kuma aka dakatar da mahimman taruka dabam dabam.   Da yake bikin zagayowar ranar haihuwara a jiya Lahadi, inda ya cika shekaru 27, Pogba ya ce yana harin tara fam dubu 27 ne don taimakawa wajen yaki da shu’umar cutar. Pogba ya ce, yana murnar kasancewa cikin koshin lafiya a daidai lokacin da wasu ke fama da rashin lafiya, saboda haka kamata ya yi y aba da tasa gudummawar wajen nema mus...
Ighalo ya amince a zabtare albashinsa don ci gaba da zama a Manchester United

Ighalo ya amince a zabtare albashinsa don ci gaba da zama a Manchester United

Wasanni
Jaridar Mail ta rawito cewa, dan wasan Manchester United kuma dan asalin Najeriya, Odion Ighalo ya amince a zabtare Pam miliyan 6 daga cikin albashinsa domin ci gaba da zaman din-din-din a kungiyar ta Manchester United.   Dan wasan mai shekaru 30 na zaman aro ne a Manchester United daga Shanghai Shenhua ta China har zuwa karshen wannan kaka.   Sai dai dan wasan na taka rawar gani a Old Trafford har ta kai cewa, kocinsa Ole Gunnar Solskjaer na zumudin rike shi har zuwa kaka mai zuwa.   Ighalo ya zura kwallaye hudu daga cikin wasanni takwas da ya buga wa kungiyar. Yanzu haka, dan wasan na karbar Pam dubu 240 a kowanne mako a Shanghai, amma rahotanni sun ce, a shirye yake ya rage kashi 50 na wannan albashin domin ci gaba da zama a Manchester United. ...
Tawagar Liverpool ta fi kowacce darajar a kwallon kafa>>CIES

Tawagar Liverpool ta fi kowacce darajar a kwallon kafa>>CIES

Wasanni
Tawagar Liverpool ce ta fi ko wacce tsada a kasuwar musayen 'yan wasa tsakanin manyan Gasannin Turai biyar, kamar yadda binciken kungiyar CIES da ke bibiyar kwallon kafa ya bayyana.   Liverpool ta haura takwararta ta Premier Manchester City da yawan kudin da suka kai yuro biliyan 1.4, wanda suka yi daidai da fam biliyan 1.27, yayin da Man City take da fam biliyan 1.24, kuma take matsayi na biyu a jerin.   Chelsea ce ta biyar a jadawalin, yayin da Manchester United da Tottenham ke cikin jerin kungiyoyi goman farko.   Da jumlar darajar kudi da suka kai fam miliyan 33.7 kungiyoyin Bundesliga su ne a karshen jadawalin.   Liverpool da ke jan ragamar Gasar Premier na bukatar cin wasa biyu ne kawai cikin wasa taran da ya yi ragowa a gasar domin ta lashe t...
Girgizar kasa ta afkawa garin da Ronaldo ke kebance saboda Coronavirus/COVID-19

Girgizar kasa ta afkawa garin da Ronaldo ke kebance saboda Coronavirus/COVID-19

Wasanni
Tauraron dan kwallon kasar Portugal me bugawa kungiyar Juventus wasa, Cristiano Ronaldo da a yanzu yake can mahaifarshi, tsibirin Madeira dake kasar Portugal inda ya ware kansa dan gudun Coronavirus/COVID-19 ya sake gamuwa da wani Ibtila'I.   Ronaldo ya je duba mahaifiyarsa wadda ta samu cutar shanyewar bangaren jiki, daga nan kuma sai Maganar cutar Coronavirus/COVID-19 ta taso wanda hakan yasa dole ya ware kansa.   A Ranar Lahadi din data gabata, garin na Madeira ya fuskanci girgizar kasa da ta kai mata kin awo 3.5   Saidai bata yi tsanani ba yanda zata wa mutane barna.
Barcelona na rawar jikin sayen Neymar bayan da PSG ta rage masa Kudi

Barcelona na rawar jikin sayen Neymar bayan da PSG ta rage masa Kudi

Wasanni
PSG ta yanke wa neymar farashi gami da tambayar da ake mata akan dan wasan. Marca tace Neymar yana kokarin komawa Barcelona  ayayin da kulob din Paris saint German ta yanke mai farashin Euros miliyan 150 saboda suna tsammmanin zai bar kulob din su. Darektan wasan kulob din Leonardo, ya yanke shawarar cewa zasu iya barin Neymar ya bar kulob din a karo na farko amma ba zasu taba barin Kylian Mbappe ya bar kulob din ba. An samu labarin ne daga wajen dan jarida mai suna Julian Laurens na ESPN, euros miliyan 150 da PSG ta yanke wa neymar tayi kadan akan yadda yan Barcelona da lauyoyin Neymar suke tunani saboda sun buga FiFA shekarar data wuce kuma ya kai tsawon shekaru 3 a kulob din kuma ace basu Kara mai farashi ba. Barcelona sun ci gaba da duba da wannan lamarin cewa, Abun...
Ronaldo ya ware Otaldinshi da daukar likitoci dan kula da masu cutar Coronavirus kyauta

Ronaldo ya ware Otaldinshi da daukar likitoci dan kula da masu cutar Coronavirus kyauta

Wasanni
Rahotanni daga kasar Portugal na cewa tauraron dan kwallon kasar me bugawa kungiyar Juventus wasa, Cristiano Ronaldo ya ware daya daga cikin mayan otal dinshi dan yin amfani dashi wajan kula da masu cutar Coronavirus.   Hakan ya fitone a Rahoton Marca inda aka ruwaito cewa Ronaldo zai yi hakanne kyauta kuma zai dauki kwararrun likitoci dan yin wannan aiki.  
Ronaldinho ya ci kwallaye 5 a gidan yarin da ake tsare dashi a kasar Paraguay: Messi ya karyata cewa zai taimaka masa

Ronaldinho ya ci kwallaye 5 a gidan yarin da ake tsare dashi a kasar Paraguay: Messi ya karyata cewa zai taimaka masa

Wasanni
Tauraron dan kwallon Brazil da Barcelona, Ronaldinho dake tsare a gidan Maza na kasar Paraguay na cikin annashuwa dan kuwa har ya buga kwallo kuma yayi nasara.   Hukumomin kasar Paraguay sun kama Ronaldinho inda suka daureshi a gidan yari shi da dan uwansa bayan kamasu da laifin shiga kasar da takardun bizar Bogi.   Saidai lauyan dan wasan me shekaru 39 ya bayyana cewa Ronaldinho bai san cewa fasfon bogine aka bashi ba, yace ya kamata ace hukumar kasar ta lura da wannan abu.   An bada belin Ronaldinho akan Yuro Miliyan 4 saidai har yanzu yana tsare dan babu wanda yayi belin nasa.   An ruwaito cewa tsohon abokin wasansa, Messi yayi yunkurin ceto dan wasan saidai na kusa da Messin sun karyata wannan zargi inda suka ce Messi baiji dadin abinda ya fa...
Coronavirus/COVID-19: Juventus ta killace mutane 121

Coronavirus/COVID-19: Juventus ta killace mutane 121

Wasanni
Dan wasan baya Daniele Rugani shine dan wasan Serie A daya fara kamuwa da cutar Covid-19 kuma ya kasance daya daga cikin yan kulob din juventus  wanda suka hada dakin canja kaya daya da sauran yan wasan bayan sun yi nasarar wasan su da inter Milan. Yan kungiyar sun ce bayan jiya an tabbatar da cewa Rugani yana dauke da cutar Covid-19, Hakan yasa yan kungiyar guda 121 suka taimaka suka killace kansu da kansu kamar yadda doka ta tanadar kuma sun hada da yan wasan su da ma'aikatan su da da jami'an tsaro masu rakiya. Duk da cewa an ruwaito abokin aikin Rugani ya kamu da cutar coronavirus wato Dybala kasar Argentina ta karyata cewa bai kamu da cutar ba. Dan wasan a shafinsa na Twitter ya bayyana cewa inaso in tabbatar wa mutane cewa lafiyata kalau nagode da sakonnin ku da fatan kuma k...