Saturday, June 6
Shadow

Wasanni

Ronaldo ya ware Otaldinshi da daukar likitoci dan kula da masu cutar Coronavirus kyauta

Ronaldo ya ware Otaldinshi da daukar likitoci dan kula da masu cutar Coronavirus kyauta

Wasanni
Rahotanni daga kasar Portugal na cewa tauraron dan kwallon kasar me bugawa kungiyar Juventus wasa, Cristiano Ronaldo ya ware daya daga cikin mayan otal dinshi dan yin amfani dashi wajan kula da masu cutar Coronavirus.   Hakan ya fitone a Rahoton Marca inda aka ruwaito cewa Ronaldo zai yi hakanne kyauta kuma zai dauki kwararrun likitoci dan yin wannan aiki.  
Ronaldinho ya ci kwallaye 5 a gidan yarin da ake tsare dashi a kasar Paraguay: Messi ya karyata cewa zai taimaka masa

Ronaldinho ya ci kwallaye 5 a gidan yarin da ake tsare dashi a kasar Paraguay: Messi ya karyata cewa zai taimaka masa

Wasanni
Tauraron dan kwallon Brazil da Barcelona, Ronaldinho dake tsare a gidan Maza na kasar Paraguay na cikin annashuwa dan kuwa har ya buga kwallo kuma yayi nasara.   Hukumomin kasar Paraguay sun kama Ronaldinho inda suka daureshi a gidan yari shi da dan uwansa bayan kamasu da laifin shiga kasar da takardun bizar Bogi.   Saidai lauyan dan wasan me shekaru 39 ya bayyana cewa Ronaldinho bai san cewa fasfon bogine aka bashi ba, yace ya kamata ace hukumar kasar ta lura da wannan abu.   An bada belin Ronaldinho akan Yuro Miliyan 4 saidai har yanzu yana tsare dan babu wanda yayi belin nasa.   An ruwaito cewa tsohon abokin wasansa, Messi yayi yunkurin ceto dan wasan saidai na kusa da Messin sun karyata wannan zargi inda suka ce Messi baiji dadin abinda ya fa...
Coronavirus/COVID-19: Juventus ta killace mutane 121

Coronavirus/COVID-19: Juventus ta killace mutane 121

Wasanni
Dan wasan baya Daniele Rugani shine dan wasan Serie A daya fara kamuwa da cutar Covid-19 kuma ya kasance daya daga cikin yan kulob din juventus  wanda suka hada dakin canja kaya daya da sauran yan wasan bayan sun yi nasarar wasan su da inter Milan. Yan kungiyar sun ce bayan jiya an tabbatar da cewa Rugani yana dauke da cutar Covid-19, Hakan yasa yan kungiyar guda 121 suka taimaka suka killace kansu da kansu kamar yadda doka ta tanadar kuma sun hada da yan wasan su da ma'aikatan su da da jami'an tsaro masu rakiya. Duk da cewa an ruwaito abokin aikin Rugani ya kamu da cutar coronavirus wato Dybala kasar Argentina ta karyata cewa bai kamu da cutar ba. Dan wasan a shafinsa na Twitter ya bayyana cewa inaso in tabbatar wa mutane cewa lafiyata kalau nagode da sakonnin ku da fatan kuma k
Coronavirus/COVID-19: An killace Messi

Coronavirus/COVID-19: An killace Messi

Wasanni
Kungiyar kwallon kafa ta Barceona ta bayyana cewa 'yanwasanta gaba daya ciki hadda Lionel Messi an killace su inda kowa ya zauna a gida saboda fargabar Coronavirus/COVID-19.   Messi na zaune a gidanshi na alfarma me dauke da filin wasa da kudiddifin Ninqaya da dakin motsa jiki.   Ana sa ran Messi zai rika motsa jiki a cikin gida  nashi dan ya kasanceda kuzari
Hukumar wasannin kwallon kafa ta Jamus  DFL ta dakatar da wasannin Bundesliga

Hukumar wasannin kwallon kafa ta Jamus DFL ta dakatar da wasannin Bundesliga

Wasanni
Hukumar wasannin kwallon kafa ta Jamus DFL ta dakatar da wasannin Bundesliga har zuwa ranar biyu ga watan Afrilu. A karon farko a tarihin wasannin Bundesliga na Jamus a wannan makon an gudanar da wasanni ba tare da 'yan kallo a filayen kwallo ba. A waje guda kuma mahukunta sun ce an jingine wasannin a sakamakon tsoron yaduwar cutar Coronavirus. Dakatar da wasannin ya shafi har da wasannin da aka shirya gudanarwa a karshen makon nan. Rahoto daga DW Jamus
An dakatar da gasar Premier League saboda Coronavirus/COVID-19

An dakatar da gasar Premier League saboda Coronavirus/COVID-19

Wasanni
Hukumar kwallon kafa ta kasar Ingila tace an dakatar da wasannin gasar Premier League na kasar dama duka sauran wasu wasannin da ake bugawa.   Dakatarwar ta hada da gasar wasannin mata dadai sauransu.   Hakanan hukumar ta bada shawarar daina duk wasu aikace-aikace na kungiyoyi da suka hada da haduwar  yan wasa a guri daya da ganawa da masoya da kuma masu ziyarar bude ido.
An dakatar da gasannin Champions League da Europa

An dakatar da gasannin Champions League da Europa

Wasanni
An dage duka gasannin UEFA, har da wasannin da za a yi a gasannin zakarun Turai na Champions League da Europa ran 17 da 18 ga wannan watan na Maris, saboda barkewar coronavirus. Haka kuma na dakatar da fitar da jadawalin wasannin da za a buga, wanda da za a yi a 20 ga watan Maris. An dage wasannin da za a yi tsakanin Manchester City da Real Madrid, da kuma Juventus da Lyon, da kuma Barcelona da Napoli da kuma tsakanin Bayern Munich da Chelsea a gasar Champions League a makon gobe. An soke wasannin Manchester United da Wolves da Rangers a gasar Europa kamar yadda suka wallafa a shafinsu na Twitter.
Dan wasan Chelsea, Hudson-Odoi ya warke daga Coronavirus/COVID-19

Dan wasan Chelsea, Hudson-Odoi ya warke daga Coronavirus/COVID-19

Wasanni
Tauraron matashin dan kwallon kungiyar Chelsea,  Callum Hudson-Odoi ya taki sa'a inda cikin awanni 24 da tabbatar da cewa ya kamu da cutar Coronavirus/COVID-19 tuni har ya warke.   Dan wasan me shekaru 19 ne da kansa ya fito ta shafinshi na sada zumuntar Twitter ya gayawa Duniya cewa ya warke kuma kwanannan zai dawo aiki.   https://twitter.com/Calteck10/status/1238374982289424384?s=19
An dakatar da wasan kwallon kafa na Faransa ‘har sai zuwa wani lokaci,

An dakatar da wasan kwallon kafa na Faransa ‘har sai zuwa wani lokaci,

Wasanni
An dakatar da wasan kwallon kafa na Faransa "har sai an sanarda shi" saboda barkewar cutar coronavirus, majiyoyin dake kusa da LFP, wadanda ke kan gaba a rukunin Ligue 1 da Ligue 2, sun fada wa AFP ranar Juma'a.   Majiyar ta ce ta dauki matakin "baki daya" na dakatar da wasan ba tare da wani bata lokaci ba, bayan sakamako, taron da aka kira na gaggawa da akayi a ranar Juma'a. Inda aka amince da tsaida wassanin har zuwa wani lokaci.