Wednesday, June 3
Shadow

Chelsea sun karawa Giroud tsawon kwantirakin shi

Giroud ya kusa barin kungiyar Chelsea yayin da aka bude kasuwar yan wasan kwallon a watan janairu, amma ya fasa saboda Frank Lampard ya kasa samun dan wasan da zai maye gurbin shi.

Oliver Giroud ya samu damar shiga tawagar yan wasa 11 na farko a kungiyar Chelsea bayan Tammy Abraham ya samu rauni,kuma Giroud yana kokari sosai kafin a dakatar da wasannin kwallon kafa.

 

Giroud yana cikin yan wasan da kwantirakin su zai kare a wannan kakar wasan amma yanzu an kara mai zuwa kakar wasan 2020/2021. Shima golan su Willi Cabellero an kara mai shekara daya yayin su kuma Pedro da Willian har yanzu ba’a kara masu ba.

 

Giroud yace yana jin dadi saboda zai cigana da wasa a kungiyar Chelsea kuma yana so ya ga yasa kayan Chelsea a filin wasan su musamman a gaban masoyam su gabadaya idan an basu damar yin hakan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *