fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Chelsea sun samu matsala da kochin su Lampard akan maganar siyan Timo saboda Aubameyang

Kungiyar Chelsea suna harin siyan tauraron dan wasan RB Leipzig Timo Werner wanda aka sawa farashin euros miliyan 53 amma sai dai ba kowa bane ya amince da wannan maganar ba a kungiyar.

Babban kochin kungiyar Frank Lampard da mai bada shawara Peter Cech sun bukaci kungiyar da su siya dan wasan Arsenal Pierre Emrick Aubameyang, yayin da Arsenal zasu siyar da dan wasan a farashi mai sauki saboda watanni 12 ne suka rage mai a kungiyar.
Chelsea sun yi yunkurin siyan Abameyang a watan janairu amma Arsenal basu amince ba, yanzu kuma sun shirya siyar da dan wasan nasu a karshen wannan kakar wasan. Abameyang ya kasance babban dan wasan da Lampard yake so ya siya a yanzu.
Shima Timo yana cikin yan wasan da Lampard yake harin siyan amma ya bayyana cewa ya fi son kwararren dan wasa mai cin kwallaye kamar Aubameyang. Yayin da aka samu labari cewa Chelsea sun cigaba da tattaunawa gami da maganar Timo Warner.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Shalelen PSG, Mbappe ya samu sabani da Messi kan sayar da Neymar a wannan kakar

Leave a Reply

Your email address will not be published.