Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta lallasa Liverpool da ci 2-0 a wasan da suka yi na neman daukar kofin FA Cup a daren yau.
Wannan sakamakon na nufin an fitar da Liverpool daga gasar ta FA Cup.
Tun kamin a tafi hutun rabin lokaci Willian ya sakawa Liverpool kwallo a raga wadda ta makale. Hakanan bayan dawowa daga hutun rabin lokacin, Barkley ya kara kwallo ta 2 wanda a haka aka tashi wasan.
KEPA SAVES 👏
KEPA SAVES 😳
KEPA SAVES 🤯#UndertheLights #CHELIV pic.twitter.com/RBIedbfnoS— The Emirates FA Cup (@EmiratesFACup) March 3, 2020
Golan Chesea, Kepa Arrizabalaga yayi bajinta sosai saboda taren da yayi a wasan inda yayi ta shan yabo.
Hakanan matashin dan wasa me shekaru 18, Billy Gilmour shima yayi bajinta sosai inda shine ma ya lashe kyautar gwarzon wasan na yau.
— Zwoddebck (@zwoddebck) March 3, 2020
Ya yiwa Fabinho wata yanka da akaita magana akanta
Billy Gilmour vs Fabinho. Generational talent pic.twitter.com/f7oGm5Fhrk
— P5 ⭕️ (@ParisCFC) March 3, 2020
Hakanan shima Giroud ya barar da wata dama me kyau data dauki hankula sosai.
https://twitter.com/EmiratesFACup/status/1234953724554043397?s=19