fbpx
Friday, July 1
Shadow

Chelsea zasu rasa Christian Pulisic in har suka siya Philippe Coutinho

An shawarci kungiyar Chelsea cewa ba sai sun siya Coutinho ba a wannan kakar wasan saboda suna da dan wasan dake buga masu lamba 10. Daya daga cikin masu sharhi na ESPN Don Hutchison yace Chelsea zasu rasa Christian Pulisic in har suka siya dan wasan Brazil din.

Chelsea suna samun nasara wurin siyan dan wasan Brazil din yayin da Bayern Munich suka fasa siyan shi bayan sun aro shi daga kungiyar Barcelona. Barcelona suna kokarin siyar da dan wasan domin su samar ma Neymar da Lautaro Martinez matsugunni a kungiyar duk da cewa bai zama lallai su siya gabadaya yan wasan ba.
Hutchison yana gargadin Chelsea gami da siyan Philippe coutinho da suke so suyi saboda zasu rasa Christian Pulisic.
Dan wasan amurikan Pulisic ya shiga kungiyar Chelsea ne a kakar wasan bara a farashin euros miliyan 57 amma baya kokari sosai. Yayin da yayi nasarar cin kwallaye guda biyar kacal a wasanni guda 16 daya buga a wannan kakar wasan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Za'a ba wanda ya lashe gasar tseren Marathon dala 80,000 a jihar Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published.