fbpx
Monday, June 27
Shadow

Chukuma Soludo: Tilas ne ‘yan Arewa su yi zamansu a Kudu kamar yadda Igbo ke zaune a Arewa

Al’ummar Musulmi mazauna Jihar Anambra sun yi wata ganawa da gwamnan jihar, Farfesa Chukuma Soludo, bayan kisan gillar da aka yi wa wata mata Musulma da ‘ya’yanta hudu a jihar, abin da ya jawo Allah-wadai daga ko ina a kasar.

A wani sakon da ya saka a shafinsa na Twitter Gwamna Soludo ya ce ganawarsa da Shugabannin Musulmin Anambra ta yi matukar wayar masa da kai.

BBC ta tuntubi Garba Haruna, Sarkin Hausawan Birnin Awka, daya daga cikin wadanda suka halarci taron domin jin karin bayani kan abubuwan da aka tattauna.

Ga abin da ya ce ya fi damun al’ummar arewacin kasar mazauna Jihar: “Abubuwan da suke damunmu su ne na rashin tsaro yadda ake samun mutanenmu ake musu kisan-gilla. A takaice abin da muka sanar da Gwamna Soludo ke nan. Shi ma kuma ya ce wannan matsalar tamu ta dame shi matuka.”

Sarkin Hausawan Awkan ya kuma ce gwamnan Jihar ta Anambra ya yi musu alkawarin tura karin jami’an tsaro zuwa yankunan da al’ummar Arewacin Najeriya ke zama.

Ya kara da cewa, “Gwamna Soludo ya bukaci mu ci gaba da zama da yin sana’o’inmu a cikin Jihar kamar yadda muka saba, kamar yadda ‘yan kabilar Igbo da ke zaune a arewacin Najeriya ke ci gaba da zamansu lafiya. Saboda haka ya tabbatar mana da tsaro.”

Kan batun kiyaye tsaro, Sarki Garba Haruna ya ce sun yi kira ga ‘yan arewa da su guji shiga kauyukan Jihar ta Anambra har sai yanayin tsaron ya inganta.

Ya shaida wa BBC cewa akwai kananan hukumomi bakwai da ‘yan bindigan ke son mamayewa baki daya.

“Wurin na gefen garin Nnewi ne, domin Nnewi ne shalkwatar yankin. Mun sanar da shi barazanar da wasu ‘yan kabilar Igbo na wani kauye da ke cewa tilas ‘yan arewa su bar wurin. To gwamnan ya ce bayan mun kammala tattaunawa zai tafi kauyen domin sanar da su cewa ba zai bari su dauki irin wannan matakin ba.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.