Shugaban hukumar zanawa da ƙera motoci ta Najeriya, Jilani Aliyu, ya ƙaddamar da motocin bas 2,322 da aka haɗa a Najeriya waɗanda ƙungiyar direbobin haya ta RTEAN ta saya.
Ƙungiyar ta sayi motocin ne masu amfani da gas don raba su ga mambobinta a ƙananan hukumomi 774 da ke faɗin Najeriya.
Da yake ƙaddamar da motocin a Abuja ranar Juma’a, Jilani ya ce “abin alfahari ne a ce kamfanin ƙasar ne ya haɗa dukkan motocin kuma a cikin Najeriya”.
Ya ƙara da cewa: “Ina taya shugaban RTEAN, Alhaji Musa Maitakobi, murna bisa samarwa da kuma bin tsarinmu na amfani da motoci masu amfani da gas da kuma abubuwan da aka ƙera a Najeriya.”

Jilani ya kuma ce a matsayin Najeriya ta ɗaya daga cikin ƙasashen da suka saka hannu kan yarjejeniyar Paris don rage hayaƙi mai gurɓata muhalli, dole ne ƙasar ta yi amfani da arzikin iskar gas mai ɗumbin yawa da take da shi.
Daga BBChausa.