fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Cikin sauki APC zata ci zabe a shekarar 2023>>Inji Gwamnan Katsina

Gwamnan jihar katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana cewa, cikin sauki jam’iyyar su ta APC zata lashe zaben shekarar 2023.

 

Ya bayyana hakane ranar Laraba a ganwar da yayi da manema labarai a jami’ar Alhikma.

 

Yace duk masu cewa, APC ba zata ci zabeba a shekarar 2023, basu san abinda suke cewa ba.

 

Yace matsalolin dake faruwa a Najeriya yana faruwa a kasashen Duniya da dama, dan haka ba akan Najeriya ne kadai ba.

 

Yace ko da a shekarar 2019 ma haka aka rika cewa, wai APC ba zata ci zabeba, amma kuma ta ci zaben.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.