Saturday, July 20
Shadow

Cin yaji ga mai ciki

Cin abinci me yaji ga mai ciki bashi da matsala sam ko kadan. Kuma ba zai cutar da dan cikinki ba.

Saboda yanayin bakin me ciki, zaki so cin abu me yaji dan kwadayi, masana sun ce zaki iya ci ba tare da matsala ba.

Mutane da yawa na da tunanin cewa, abinci me yaji yana da hadari ga mai ciki amma hakan ba gaskiya bane.

Saidai a sani ko menene aka yishi ya wuce iyaka zai iya bayar da matsala.

Hakanan kowace mace da irin jikinta, wata Yaji zai iya zamar mata matsala, wata kuma bata da matsala dashi.

Dan haka kinfi kowa sanin kanki.

Karanta Wannan  Uba Sani ya yi wa fursunoni 110 afuwa

Yaji zai iya sa zafin kirji ko kuma rashin narkewar abinci wanda duka basu da mummunar illa ga me ciki.

Jin kwadayin cin abinci me yaji ba matsala bane ga mace me ciki, ga wasu amfanin da abincin me yaji zai yiwa mace me ciki kamar haka:

Cin abinci me yaji yana baiwa dan ciki damar dandanon yaji, yaro yakan yi sabo da abinda yake ci a cikin mahaifiyarsa. Dan haka bashi yaji tun a ciki, zai bashi damar dandanonshi kamin ya fito Duniya.

Cin abinci me yaji yana taimakawa wajan kara karfin garkuwar jiki. Kuma yana taimakawa wajan rage hadarin kamuwa da cutar zuciya ko ta shanyewar rabin jiki.

Karanta Wannan  Kalli Wani tsohon Bidiyo na Nazir Ahmad Sarkin Waka da ya dauki hankula

Matsalolin cin abinci me yaji ga mai ciki:

Kamar yanda muka ce a sama, duk amfanin abu, ana iya samun wani abu me illa a tare dashi.

Ga illolin cin abinci me yaji kamar haka:

Zafin kirji ko zuciya, dama wasu matan kan yi fama dashi amma cin yaji na karashi.

Bacin ciki, Wasu matan dama na fama da rashin narkewar abinci yayin laulayin ciki, cin abinci me yaji na kawo bacin ciki inda zai iya saki ciwon ciki da zawo da yawan tusa.

Hakanan yana sa ciwon safe ko zazzabin safe, wanda dama wasu masu cikin na fama dashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *