fbpx
Tuesday, March 28
Shadow

Cin zali: Kasar Isra’ila ta tursasawa wani kauyen falasdinawa tashi dan ginawa mutanen kasarta gidaje

hoton kauye a kasar Falasdinawa-Aljazeera
Wannan hoton wani kauyene a kasar Falasdinawa da ke shan kwacen fin karfi daga hannun kasar Isra’ila, kamar yanda kafar watsa labarai ta Aljazeera ta ruwaito dama can mutanen wannan kauye an kwace musu gurin da suke zaunene tun shekarun 1948 lokacin da aka kafa kasar Isra’ila, daga nan ne sai suka dawo nan da zama, to nan din ma gashi Isra’ilar ta biyosu, ta basu kwanaki takwas, su hada komatsansu susan inda dare ya musu.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Shidai wannan kauye yana da mutane kimanin dari uku da suke zaune a cikinshi kuma ko da ma can idan wani ya sake yayi gini a cikin garin ba tare da hukumomin kasar Isra’ila sun bashi damar yin hakan ba to zasu zo su ruguje gidan.

Shugaban kauyen ya shaidawa wakilin Aljazeera cewa ranar Alhamis data gabatane suka ga hukumomin kasar ta Isra’ila sun shigo suka buga takardar sanarwar kowa ya tashi daga garin nan da kwana takwas, in ba haka ba za’a turo jami’ai su musu korar wulakanci.
Haka dai kasar Isra’ila takewa Faladinawa wannan cin kashin na kama gurarensu suna gini a gurin da Duniya gaba daya ta yadda da cewa haramtaccene amma an kasa samun wanda zai musu magana.
Saidai mutanen garin sunce ba zasu tashi ba saidai duk yanda za’ayi ayi.
Allah shi kyauta.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Zababben dan majalisa mai shekara 34, Lawan Musa Majakura, ya bayyana yadda Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Yobe, Ahmed Mirwa Lawan, ya sa aka kama shi saboda ya caccake shi a shafin Facebook.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *