Cocin katolikawa ta jihar Ondo ta bayyana cewa za a bunne mutanen da ‘yan bindiga suka kashe a cocin katolik dake karamar hukumar Owo ranar juma’a.
Zasu gudanar da jana’izar ne a Otapete, layin Emure da misalin karfe tara na safe.
A ranar lahadi hudu ga watan yuni ne ‘yan bindiga suka kaiwa cocin mummunan hari inda suka kashe mutane dama kuma suka raunana wasu.
Cocin ta kasance a mahaifar gwamnan jihar watau Rotimi Akeredolu inda yace kimanin mutane 40 suka rasu.