Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, shi ne gwamna na bayan nan da aka gwada aka tabbatar ya kamu da cutar korona a Najeriya.
Tun da farko Gwamna Ikpeazu an masa gwajin cutar bayan ya kai kansa wajen gwajin a ranar 30 ga watan Mayu, aka kuma tabbatar da ba shi da cutar, amma bayan an kara mi shi gwaji na biyu a ranar 4 ga watan Yuni sai sakamakon ya nuna yana dauke da cutar.
Haka zalika, gwamnan ya killace kansa karkashin kulawar wani kwararren likita, wanda ya umarci mataimakinsa ya rike kujerar shugabancin kafin ya koma bakin aiki.
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed
An gwada gwmanan Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya Bala Muhammed kuma sakamakon ya nuna yana dauke da cutar a wuraren watan Maris na 2020.
Mai magana da yawun Gwamnan Muktar Gidado ta cikin wata sanarwa ya ce sai da hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta NCDC ta gwada gwamnan sau shida tukunna aka tabbatar yana dauke da cutar.
Wuraren 9 ga watan Afrilu ne Gwamna Bala Mohammed ya fada a Tuwita cewa an masa gwaji kuma ya warke daga cutar.
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El Rufai,
A ranar 29 ga watan Maris, Gwamnan Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai ya sanar da cewa yana dauke da cutar korona.
Ya kuma kara da cewa ya killace kansa kamar yadda NCDC ta ba da shawara, musamman ga mutanen da suka kamu da cutar ba tare da nuna alamu ba.
Daga baya a ranar 23 ga watan Afirilu, El-Rufa’i ya kara sanar da cewa sakamakon gwajin da aka yi masa ya nuna ba shi da cutar, bayan kusan shafe kwanaki 14 yana karbar kulawa ta musamman.
Yayin killace kansa da ya yi, El-Rufai ya ci gaba da wallafa sakon tuwita kan halin lafiyarsa tare da gudanar da wasu taruka da shuka shafi gwamnatinsa ta intanet.
Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya sanar ta shafinsa na intanet cewa an yi masa gwajin cutar korona kuma ya kamu da ita a ranar 30 ga watan Maris.
Ya kuma ce ba ya nuna alamun kamuwa da cutar amma yana ci gaba da killace kansa.
Bai dade ba sosai, a ranar 5 ga watan Afirilu gwamnan ya fito ya ce an kara gwada shi ba shi da wannan cuta, ya yi godiya ga ma’aikatan hukumar NCDC da kuma jama’ar da suka masa addu’ar samun lafiya.
Har yanzu korona na ci gaba da yaduwa a Najeriya, ya zuwa yanzu kuma akwai kimanin mutum 12,486 da suka kamu da cutar yayin da 354 suka mutu.