Ƙarin mutum 339 ne hukumomi a Najeriya suka tabbatar a ranar Alhamis sun sake kamuwa da cutar korona, kuma da wannan, adadin masu cutar ya kai 7,016.
Alƙaluman hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta Najeriya a daren Alhamis ta ce mutum 11 ne suka sake rasuwa sakamakon annobar a cikin sa’a 24. Yanzu yawan mutanen da suka mutu a Najeriya 211.
Haka zalika mutum 67 sun warke kuma an sallame su daga asibiti a ranar don haka yanzu mutanen da suka warke daga korona a ɗaukacin Najeriya 1,907.
A cikin sabbin alƙaluman da NCDC ta fitar, Legas jihar da cutar ta fi ƙamari an sake gano masu korona 139. Duka-duka tana da masu cutar 3,093.
Mutum 28 sun sake harbuwa da cutar a Kano, jihar da ta fi fama da annobar a yankin arewa, haka ma a jihar Oyo, cewar alƙaluman NCDC.
Har yanzu a hukumance cutar korona ba ta ɓulla cikin jihohin Kogi da Cross river ba, amma wasu na cewa mai yiwuwa akwai annobar cikinsu, kawai dai don ba a yin gwaji ne.
Jihar Edo an ƙara samun masu korona 25 cewar NCDC, yayin da Katsina ke biye mata da mutum 22 sabbin kamun cutar. Yanzu dai akwai mutum 303 masu fama da korona a Katsina.
A Kaduna ma mutum 18 aka ba da rahoto ranar Alhamsi sun sake kamuwa, a Jigawa mutum 225 ne yanzu suka kamu da korona bayan gano ƙarin 14 a baya-bayan nan.
Haka zalika jihohin Yobe da Filato duk an sake samun masu cutar 13 bayan gwajin da aka yi.
Shi ma babban birnin tarayya Abuja da ke bin Kano a yawan masu korona da mutum 446, bayan NCDC ta ce mutum 11 sun sake kamuwa.