Kamfanin BUA wanda attajirin dan kasuwa, Abdulsamad Rabiu ke shugabanta ya baiwa jihar Legas wadda itace ta fi kowace jiha yawan masu cutar Coronavirus/COVID-19 tallafin motocin daukar marasa lafiya 5 da tallafin kudi,Naira Miliyan Dari 2.
Da yake mika tallafin ga wakilan gwamnatin Legas, Me kula da tsare-tsaren kamfanin,Chimaobi Madukwe ya bayyana cewa suna matukar Alfahari da kasancewa suna aiki da jihar ta Legas inda yace zasu ci gaba da tallafawa a Najeriya wajan yaki da cutar.
BUA ya bayar da irin wannan tallafi a jihohin Katsina,Kano da sauransu.