fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Coronavirus/COVID-19 a jihar Kogi gaskiyace, Nasan mutum 1 data kama>>Sanata Dino Melaye

Tsohon sanatan Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa, cutar Coronavirus/COVID-19 a jihar gaskiyace.

 

An dai samu rashin jituwa tsakanin NCDC da jihar Kogi inda NCDC tace jihar ta Kogi ta samu mutane 2 na farko da suka kamu da cutar amma jihar tace ba gaskiya bane.

A sanarwar da ya fitar, Melaye ya bayyana cewa daya daga cikin mutanen da cutar ta kama a jihar yana garin Kabba ne kuma daga asibitin Lokoja aka aikashi zuwa Abuja.

 

Yace yasan mutumin kuma yana fatan wanda suka yi ma’amala dashi zasu mika kansu dan a musu gwaji. Yace ba zai zama cikin masu wasa da rayuwar jama’arsu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.