fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Coronavirus/COVID-19 jarabawace daga Allah>>Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2019, Alhaji Atiku Abubakar ya baygana cewa cutar Coronavirus/COVID-19 jarabawace daga Allah.

A cikin sakon daya fitar na barka da Sallah ga ‘yan Najeriya Atiku ya kuma jawo hankalin shuwagabanni da su fifita kula da jam’a a mulkinsu.

 

Ya bayyana cewa kare lafiyar mu data wanda ke tare samu na da muhimmanci dan haka ya jawo hankulan mutane da su bi dokar da hukumomi ke sakawa.

 

Yace an yi Azumi ba tare da Sauran ibadun da aka saba yi na sallar Asham ba da kuma cin abinci cikin jama’a da tafsir ba amma hakan bai sakawa Azuminmu rauni ba dan kuwa mun san cewa duk waji yanayi da muka tsinci kan mu a ciki daga Allah ne kuma dama Allah yayi Alkawarin gwada imanin mu.

Karanta wannan  Dattawan Arewa sun gargadi Atiku cewa kar ya canja Okowa a matsayin abokin takararsa

 

A karshe Atiku ya taya Musulmai murnar Sallar inda yayi fatan za’a yi ta cikin farin ciki tare da iyalai.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.