fbpx
Saturday, January 16
Shadow

Coronavirus/COVID-19 karyace, ku kiyaye amfani da takunkumin rufe baki da hanci>>Inji Farfesoshin jami’ar dake jihar Delta

Farfesa Cyril Otoohhiaus na jami’ar Novena dake Ogume, jihar Delta ya bayyana cewa cutar Coronavirus/COVID-19 karyace.

 

Ya kara da cewa cutar a dakin bincike aka kirkireta dan a tashi kudi daga Nahiyar Africa. Farfesan ya bayyana hakane a wajan wani taron wayar da kai kan cutar Coronavirus/COVID-19 da aka yi a jihar Kogi,kuma yayi wanna bayanine a gaban gwamnan jihar,Yahaya Bello.

 

Ya kara da cewa saboda cutar ta karyace shiyasa gashinan ita kanta hukumar lafiya ta Duniya, WHO ta kasa bayyana alamomin cutar na Ainahi, duk ta rude.

 

Ya kara ds cewa wanine kawai ya zauna ya kirkiri cutar da kansa shiyasa WHO ta kasa amsa tambayoyi da yawa akan cutar.

 

Shima dai Farfesa Josiah Adjene da yayi bayani a wajan taron ya bayyana cewa mutane su yi hankali da yawan amfani da takunkumin rufe fuska inda yace yana rage yawan iskar da jiki ke bukata.

 

Yace kuma yawan amfani dashi akai-akai zai iya haifarwa da mutum matsala a gaba. Ya bayyana cewa duk alamomin cutar Coronavirus/COVID-19 da ake bayyanawa dama can akwaisu a Africa ba sabon abu bane.

 

Ya kuma baiwa jihar Kogi shawarar saka jari a harkar noma ta yanda zata ciyar da Najeriya nan gaba bayan maganar cutar Coronavirus/COVID-19 ta wuce.

 

Da yake magana a wajan taron, Gwamna Yahaya Bello ya bayyana cewa ya kira wannan taronne dan a wayarwa da jama’ar jiharsa kai kan batun cutar Coronavirus/COVID-19.

 

Yace Najeriya da jihar Kogi na cikin takura saboda batun cutar Coronavirus/COVID-19.

 

Har yanzu dai jihar Kogi bata samu koda mutum 1 me dauke da cutar ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *