Sunday, June 7
Shadow

Coronavirus/COVID-19: Ronaldo da Messi sun yadda su karbi ragin albashin da aka musu

An dakatar da wasan kwallon kafa saboda akwai wani babban al’amari daya fi wasan, kuma ba wani abu bane illa cutar coronavirus. Kuma abun alfahari ne ace babban dan wasa kamar Cristiano Ronaldo yana yin iya bakin kokarin dan yaga ya taimakawa kulob din shi.

An samu labari bada dadewa ba cewa Messi ya yadar zai karbi ragin albashi a kasar Spain, kuma ganin hakan ne yasa Cristiano Ronaldo yace shima yace zai karbi ragin albashin. Dan wasan portugal din ya karyata wannan labarin cewa shi bai canja ra’ayin shi saboda da Messi ba.
An samu labari daga tutusport cewa Ronaldo zai karbi ragin albashin euros miliyan 3.8 a kowace shekara saboda ya taimakawa kungiyar ayayin da duniya take cikin rikicin cutar coronavirus.
A kowane mataki mutun yake, abun alfahari ne ace a yau zakarun yan wasan kwallon kafa na duniya har guda biyu sun ce “kudi bakomai bane a wurin su”.
Ronaldo ya samu duk wani abu a ake bukata a kwallon kafa, ya ci abubuwa dayawa kuma ya samu karramawa daga wurin mutane, kungiyoyi dakuma duniya baki daya. Kuma zai kasance daya daga cikin jiga-jigan yan wasan kwallon kafa a kowane lokaci.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *