fbpx
Monday, August 8
Shadow

Coronavirus/COVID-19 ta kashe mutane fiye da Miliyan 1 a Duniya

Cutar korona ta halaka mutum fiye da miliyan daya, a cewar masu bincike, suna masu cewa yankuna da dama na duniya suna bayar da rahotannin ta’azzarar cutar.

Alkaluman Jami’ar Johns Hopkins sun nuna cewa cutar ta fi kisa a Amurka, Brazil da kuma India inda kasashen uku ke da rabin mutanen da cutar ta kama a duniya baki daya.

Masana sun bayyana cewa yaan mutanen da cutar ta kama ya fi wanda ake bayar da rahoto.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin duniya António Guterres ya bayyana adadin mutane da cutar ta kashe a matsayin wani abu “mai gigitarwa”.

Karanta wannan  Ba zamu roki kungiyar malamai ta ASUU ta janye yajin aiki ba, iyayen dalibai suka mayarwa gwamnatin tarayya martani

“Dole mu yi la’akari da mutanen da cutar ta halaka,” a cewarsa a sakon bidiyon da ya fitar.

“Su iyaye ne maza da mata, matan wasu ne, mazajen wasu ne, ‘yan uwan wasu ne, sannan abokai da kawayen wasu ne.”

Lamarin ya faru ne watanni 10 tun bayan barkewar cutar wadda ta samo asali daga birnin Wuhan na kasar China.

Cutar ta watsu zuwa kasashe 188 inda fiye da mutum miliyan 32 suka kamu da ita.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.