fbpx
Monday, August 8
Shadow

CORONAVIRUS: Kotu Ta Bada Belin Limamai Uku Da Suka Yi Sallar Juma’a A Jihar Kaduna Akan Naira Milyan Daya-Daya

Wata kotun majastare dake layin Ibrahin Taiwo, a Kaduna ta bada belin wasu Limamai 3 da suka gudanar da sallar Juma’a, duk da dokar hana zirga zirga da aka sanya a Kaduna a daidai lokacin.

 

 

An bada belin Muhammad Umar, wanda ake zargin ya karya dokar gwamnatin jihar na hana zirga zirga don dalkile yaduwa cutar corona virus.

 

 

An bada belin Umar ne tare da limamai Yusuf Hamza, Muhammad Ubale, da Auwal Shuaibu, wadanda ke zaune a unguwan Kanawa dake Kaduna, ana zargin su ne da laifin hada baki da bijirewa da dokar gwamnatin jahar.

 

 

Alkali Ibrahim Musa, ya kuma bayar da belin Hamza, Ubale da Shuaibu suma akan kudi Naira Miliyan 1 kowannne su.

 

 

Alkali musa ya kuma bukaci su samu wani sananne dake zaune a garin Kaduna don ya tsaya musu.

 

 

“Zan tura ku zama a wajen ‘yan sanda maimakon gidan yari har sai kun ciga sharuddan dake tattare da belinku, na yi haka ne saboda cutar coronavirus”, inji Alkalin.

 

 

“Dole wanda zai tsaya muku ya zama ma’aikacin gwamnati mai matakin albashi 14, zai kuma gabatar wa kotu da takardar asusun ajiyar bankinsa wanda ke nuna yana da ajiyar kudi da suka haura Naira Miliyan 1.

 

 

Tun da farko, mai gabatar da kara na jihar Kaduna, Bayero Dari, ya bayyana wa kotun cewa, laifin da wandanda ake zaigin suka aikata ya sabawa sashi na 59 da 115 da dokokin manyan laifuka na jihar Kaduna.

 

Ya kuma kara da cewa, a ranar 29 ga watan Maris ne da misalin katfe 4.30 na yamma aka kawo Kes din zuwa sashin binciken manyan laiffuka a rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna daga ofishin ‘yan sanda na yankin Kawo dake cikin garin Kaduna.

 

 

“Mun samu bayanin cewa, a ranar 27 ga watan Maris ne wandanda ake zargin Limamin unguwar Kanawa dake Kaduna, Malam Muhammad Umar, ya jagoranci wadanda ake zargi su uku da kuma wasu mutum 17 inda suka gabatar da sallah Juma’a (Azahar), wanda hakan ya saba wa dokar hana zirg-zirga wadda aka kafa don dakile bazuwar cutar coronavirus.

 

 

Daga na kuma ya bukaci kotu ta daga karar don su samu dammar gabatar da shaidu.

 

 

A jawabinsa, lauyan wadanda ake karar, Abdulbasit Sulaiman, ya roki kotu da bayar da belin mutanen kamar yadda dokar kasa ta tanada.

 

“Ina rokon kotu ta bayar da belin wadanda nake tsayawa kamar yadda sashi na 35 da 36 (5) na kundin tsarin mulkn shekarar 1999 ya tanada.

 

 

“Mun yi alkawarin za su kasance da kyawawan halaye kuma ba za su tsoma baki cikin binciken da ake yi ba,” inji Sulaiman.

Rariya

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.