fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Coronavirus: Mutane 5 aka sallama, 14 suka kamu a Kano

Rahotanni daga jihar Kano sun bayyana cewa an sallami karin mutane 5 da suka warke daga cutar Coronavirus a jiya,Laraba wanda hakan ya kawo jimullar yawan wanda suka warke daga cutar kuma aka sallamesu a jihar zuwa 79.

 

Saidai an samu karin mutane 14 da suka kamu da cutar a jiya wanda hakan ya kawo yawam wanda cutar ta kama a jihar zuwa 707.

 

Wani abin farin ciki shine, bayan shafe kusan kwanaki 3 a jere ana samun wanda cutar ta kashe a Kano,a jiya kuma babu wanda ta kashe, kamar yanda ma’aikatar lafiya ta jihar ta bayyanar.

Gwamnatin jihar dai na iya bakin kokarinta wajan ganin ta kawar da cutar, kamar yanda gwamna Ganduje ya fada.

Leave a Reply

Your email address will not be published.