Wednesday, June 3
Shadow

Coronavirus: Ngolo Kante ya shirya rasa sauran wasannin Premier lig saboda yana tsoro

Anba dan wasan faransan damar yin atisayi a gida kuma babban kochin kungiyar Frank Lampard ya bashi goyon baya tare sauran shugabannin kungiyar.

Kante yaje filin atisayin Chelsea ranar talata amma bai kara komawa ba saboda yana tsoro, Amma dan wasan mai shekaru 29 ya koma ranar alhamis domin ayi mai gwajin cutar coronavirus a karo na biyu.
Kante ya rasa dan uwan shi a shekara ta 2018 kafin a fara buga gasar kofin duniya saboda yana fama da ciwon zuciya, bayan wasu makonni shima Kante ya suma a filin atisayi daga baya kuma aka tabbatar mai cewa yana da cikakkiyar lafiya.
Troy Deeney da Danny Rose suma suna shakka aka dawowa saboda ofishin masu kididdiga na kasa sun samar cewa mutane masu bakar fata zasu fi mutawa dalilin Cutar Covid 19 akan masu farar fata.
Chelsea sun shirya buga sauran wasanni su guda 9 ba tare da Kante ba idan cigana da buga gasar Premier lig.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *