fbpx
Tuesday, September 29
Shadow

Coronavirus: Premier lig zasu yi gwajin cutar Covid-19 karo na biyu a yau ranar juma’a

Kanfanin fasahar binciken halittun da aka ba kwantirakin gwajin yan wasa da kuma ma’aikatan premier lig sun bayyana cewa gwajin yana daukar awanni 48 kafin a bayar da sakamako, Amma suna sa ran za’a bayar da sakamakon cikin karshen wannan makon.

Sababbin mutanen da suka kamu kawai premier lig zasu sanar tare da gwajin farko na Norwich City saboda sune kadai ba’a fadi sakamakon gwajin su na farko ba. Za’a iya yiwa kowace kungiya kusan gwajin 100 a mako saboda sau biyu suke yin gwajin wanda hakan ne ya basu damar cigaba da atisayi.
Bayan anyi gwajin farko,  Premier lig sun sanar cewa mutane 6 sun kamu da cutar Covid-19 a ranar talata daga kungiyoyi uku bayan anyi gwaji guda 748.
Ba za’a fadi sakamakon gwajin ba tare da wa’yanda suka kamu ba saboda sai sun killace kansu na tsawon kwanaki bakwai.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *