fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Coronavirus: Sai a watan Satumba zamu bude makarantunmu>>Kasar Italiya

Kasar Italiya wadda na daya daga cikin kasashen dake gaba-gana da cutar Coronavirus/COVID-19 ta fi yiwa Illa a Duniya ta bayyana cewa sai nan da watan Satumba zata bude makarantunta.

 

Mutane akalla Dubu 26 ne suka Mutu asanadin cutar a kasar wanda hakan ke nufin itace kasa ta 2 a Duniya da cutar tafi yin kisa bayan kasar Amurka.

 

A jiya,Lahadi mutane 260 ne suka rasu sanadin cutar a kasa wanda rabon da mutane kalilan haka su mutu sandin cutar tun Ranar 14 da watan Maris da ya gaba.

 

Sannan hakan ci gaba ne idan aka kwatanta da mutane 415 da suka mutu a Ranar Asabar din data gabata a kasar.

Karanta wannan  Hotuna: Kungiyar kiwon lafiya ta kaiwa shugaba Buhari ziyara a fadarsa

 

Firai ministan kasar, Giuseppe Conte ya bayyana cewa nan da Ranar Litinin, 4 ga watan Afrilu zasu bude masana’antunsu su fara aiki.

 

Saidai yace sauran kasuwancin dake tara jama’a kamar gidajen abinci da kananan shaguna sai nan gaba tukuna.

 

Ya kuma ce makarantu kuwa sai watan Satumba kamin su sake budesu, kamar yanda Daily Mail ta ruwaito.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.