Friday, May 29
Shadow

Coronavirus: Za’a fara yanka Namun dajin dake gudan Zoo dan ciyar da wasu a Kasar Indonesia saboda rashin Abinci

A kasar Indonesia rahotanni sun bayyana cewa gidan Zoo, watau na Namun daji na Badung zai fara yanka wasu dabbobin dan ciyar da wasu saboda abinci ya fara karewa.

 

Masu kula da gidan namun dajin sun bayyana cewa suna samun a kalla Dala 81,744 a duk wata amma saboda zuwan cutar Coronavirus/COVID-19 duk komai ya tsaya.

Sunce yanzu tallafine suke nema wajan ciyar da namun dajin, kuma abincin da suke baiwa Namun dajin ya Ragu sosai.

 

Reuters ta ruwaito cewa dan haka gidan Namun dajin zai fara sayanka wasu dabbobin da mudamman suka tsufa suka daina haihuwa dan ciyar da matasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *