Sunday, June 7
Shadow

COVID-19: “A shirye muke mu kwashe yan Najeriya da ke son dawowa daga kasashen waje, in ji gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya tace a shirye suke su kwashe yan Najeriya da ke son dawowa daga kasashen waje.

Gwamnatin wadda ta nuna aniyarta na kwashe ‘yan Najeriya dake zaune a kasashen waje wadanda ke fatan dawowa gida sakamakon cutar COVID-19.

Ministan Harkokin Waje, Mista Geoffrey Onyeama ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin taron tattaunawa na yau da kullun na Kwamitin Shugaban Kasa kan cutar COVID-19 a Abuja.

Game da wannan, in ji shi, ma’aikatar tuni ta yi magana da ofisoshin jakadancin Najeriya zuwa kasashen waje don tantance yadda ‘yan Najeriya za su bayyana sha’awarsu.

Ya kara da cewa ofishin sa tuni ya aike da sakonni ga dukkan ofisoshin jakadanci da kuma ofisoshin da suka dace don tantance ‘yan Najeriya da ke son komawa gida saboda COVID19.

A cewar sa da zaran an gama tattara lambobin, za a duba inda ya dace.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *