fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Covid-19: An bude filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja

Filin saukar jirgin saman Nnamdi Azikiwe, dake Abuja an sake bude shi a ranar Asabar, don cigaba da zirga zirga.

Filin jirgin saman ya kuma tsaurara matakan tsaro, da nufin rage yaduwar cutar coronavirus.

Kamfanin Dillancin Labarai na (NAN), ya ba da rahoton cewa an yi tanadin kayan wanke hannu, tare da guraran gwajin, don kare mutane daga kamuwa da cutar covid-19.

Haka zalika an kuma sake tsarawa tare da shirya kujerun da suka kasance a cunkushe domin aiwatar da tsarin bada tazara juna.

Idan zaku tuna cewa Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA), a makwannin da suka gabata, ta ce filin jirgin saman zai sake budewa don cigaba da zirga zirga a ranar 27 ga Agusta, bayan daukan  watanni a rufe a sakamakon barkewar cutar Coronavirus.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *