fbpx
Sunday, February 28
Shadow

COVID-19: Ganduje yayi kira ga Buhari da ya kawo dauki jihar kano

Gwamna Umar Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya fito fili ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta fito don ceto jihar a yakin da take yi na kawar da cutar corona dake kara zama barazana a jihar.

Gwamna Ganduje ya ce, “Duk da yawan jama’ar da jihar kano ke da shi da kuma karancin karfin tattalin arziki fiye da jihar Legas, wacce ke da tasiri a fannin tattalin arziki, gwamnatin tarayya ba ta ba da wani tallafi ba yayin da cutar corona ke kara ci gaba da hauhawa.

Gwamnan ya koka da karancin wadatattun kayan aiki inda ya bayyana jihar tana bukatar tallafin gaggawa daga gwamnatin tsakiya.

Da yake jawabi yayin da ya karbi bakuncin Darakta Janar na Cibiyar yaki da Cututtuka ta Najeriya, NCDC, Chikwe Ihekweazu, wanda ya zo jihar Kano dan ganin yadda al’amura ke tafiya, Ganduje ya ce jihar na bukatar karin cibiyoyin gwaji da kuma guraran kebewa.

Hukumar NCDC ta sake nanata kudurin ta na yin aiki tare da gwamnatocin jihohi a fadin kasar don ya kar cutar.

Ihekweazu ya ce Hukumar NCDC tana aiki kafada da kafada don ganin an magance kalubalen cutar a kasar baki daya.

Ya ci gaba da cewa sun ziyarci Kano don tantance hakikanin yanayin da jihar ke fuskanta akan cutar COVID-19 a cikin jihar da kuma matakan da gwamnatin jihar ta bullo da su don magance matsalar.

Ya kara da cewa NCDC zata kirkiro hanyoyin ne domin tallafawa jihar Kano don shawo kan yaduwar kwayar cutar a jihar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *