fbpx
Thursday, July 7
Shadow

COVID-19: Gwamnatin Kano zata fara raban tallafin kayan abinci

Raban kayan tallafi ga al’ummar jihar Kano karkashin gwamna ganduje domin rage radadi ga al’ummar jihar.

Kwamitin tallafin da gwamnatin jihar Kano ta kafa na neman taimako kan bullar cutar corona ya bayyana cewa tuni tsare-tsare sunyi nisa, domin ganin an fara gudanar da rarraba kayayyakin abinci da aka tara domin tallafawa al’ummar Jihar kano, domin rage musu radadin halin da suke ciki game da cutar Covid-19.

Farfesa Muhammad Yahuza Bello shugaban jami’ar Bayaro dake kano wanda kuma shine shugaban kwamitin tallafin wanda ya bayyana hakan ga yan jarida a yayin wata tattauna da akai dashi.

Karanta wannan  Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya kai ziyara gidan yarin Kuje bayan harin 'yan Bindiga

Farfesa Bello ya kuma bayyana cewa an samu nau’in kayan abinci kimanin buhu dubu uku, da dari uku hadi da tallafin kudi da ya kai Naira miliyan dari uku da saba’in da shida, gami da shauran kayayyakin tsaftar hannu .

A cewar sa za a raba kayayyakin ga mutane dubu 50 a fadin jihar yadda ya kamata.

A karshe yayi kira da masu iko da su Kara tallafawa ga mabukata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.