Gwamnatin tarayya ta cire dokar data sanya na hana shiga jahohin kasar a sakamakon bullar cutar Coronavirus.
Sanarwar hakan na kunshe ne ta cikin bayanin da sakataran gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya gabatar ga manema labarai a taron kwamaitin yaki da cutar coronavirus da ake gabatarwa yau da kullum a birinin tarayya Abuja.
Boss Mustapha wanda shine shugaban kwamitin ya bayyana cewa matakin zai fara aiki ne daga 1 gawatan Yuni.