fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Covid-19: Gwamnatin tarayya ta zabtare al’bashin ma’aikatan tashar jirgin sama

Gwamnatin tarayya ta zabtare albashin ma’aikatan tashar jirgin sama a kasar.

Manajan Hukumar Kula da Filin Jiragen Sama na Najeriya a ranar 19 ga watan mayu 2020 ya ce rage albashin ya kasance ne a sakamakon rufe filin tashin jirgin saman sakamakon cutar Coronavirus da ta bulla a kasar.
Jaridar Daily trust ta rawaito cewa Takardar wacce Babban Daraktan Hukumar ta FAAN, MD, Musa ya sanya wa hannu, ya ce, “Muna sanar da duk wasu ma’aikatan  cewa sakamakon karancin kudaden shiga da ake samu a sakamakon  annobar cutar coronavirus hakan na yiwuwa hukumar gudanarwa bazata iya biyan cikakken al’bashin ma’aikaci ba daga watan mayu 2020.
Amma a cewar sa dazarar kudaden shiga sun inganta, hukumar zata cigaba da biyan ma’aikata hakkokin su, kamar yadda aka saba.
 
Idan zaku iya tunawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin rufe filin tashin jiragen saman kasar tun a watan Maris na shekarar 2020.
 
Haka zalika  a ranar 6 ga watan Mayu, Shugaban Kwamitin yaki da cutar coronavirus na Shugaban kasa Boss Mustapha, ya ba da sanarwar tsawaita rufe tashoshin jiragen saman kasar zuwa makwanni hudu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.