Shugabar hukumar zartaswa ta EUn, Ursula von der Leyen, ta ce kudadden zasu taimaka wajen inganta fannin lafiya da tattalin arzikin wadannan kasashen da tuni ya kara tabarbarewa a sakamakon wannan annobar.
Matakan hana yaduwar cutar a nahiyar Turai kadai ba zata iya yin tasiri ba, inji kungiyar, muddun aka bari cutar ta ci gaba da yaduwa a sauran sassan duniya.
Ba a kai ga baiyana sunayen kasashen da zasu ci gajiyar kudadden ba tukun na, amma mambobin kungiyar na ganin nahiyar Afrika ce sahun gaba saboda dangantakarta da Turai da kuma rashin ingancin tsarin lafiyar kasashen yankin.
A gobe Laraba za a kamalla tattaunawar kan yadda za a raba wadannan kudadden ga kasashe mabukata.
Cutar Coronavirus ta je fa tattalin arzikin duniya cikin wani yana yi, wanda lamarin ke Kara ta’azzara muddin dai aka kasa cimma dakile annobar cutar Covid-19 da ta zama alaka-kai ga duniya.