fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Covid-19: Najeriya ta sake samun karin mutum 661 yayinda adadin wadanda suka mutu ya kai 506

A rahoton da Hutudole ta rawaito daga cibiyar yaki da cututtuka ta Najeriya ya nuna cewa an samu karin mutum 661 wanda suka harbu da cutar coronavirus a fadin kasar.

Cibiyar yaki da Cututtuka ta Najeriya ta sanar da hakan ne a cikin wani sakon Tuwita data wallafa a ranar Asabar.

Cibiyar ta ce sabbin wadanda suka kamu da cutar sun kamu a cikin jihohi 14 ciki har da Babban birnin tarayya Abuja.

Lagos-230
Rivers-127
Delta-83
FCT-60
Oyo-51
Edo-31
Bayelsa-27
Kaduna-25
Plateau-13
Ondo-6
Nasarawa-3
Ekiti-2
Kano-2
Borno-1.

Rahoton Hutdole sun nuna cewa an gudanar da gwajin mutum akalla 111,052 yayin da aka tabbatar da mutum  12,584 wadanda suka harbu da cutar COVID-19.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *