Rundunar ‘yan sanda a jihar Delta ta cafke mutane 46 saboda karya dokar hana zirga-zirga da gwamnatin jihar ta sanya domin hana yaduwar cutar COVID-19.
Wadanda ake zargin suna daga cikin mutane 98 da ake zargi da aikata laifi da ‘yan sanda suka kama a fadin jihar kan laifuka daban-daban da suka hada da fashi da makami, kungiyar asiri, sata da kuma fyade.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Mohammed Ali , wanda ya gabatar da wadanda ake zargin a ranar Asabar ya shawarci iyaye da su gargadi’ ya’yansu game da aikata laifi.