Cibiyar dakile yaduwar cututtuka NCDC ta sake fidda sanarwar kara samun adadin mutum 490 wanda suka harbu da cutar coronavirus a fadin kasar.
Sanarwar wanda hukumar ta wallafa ta cikin shafinta dake kafar sadarwa a ranar Lahadi 28 ga watan Yunin shekara ta 2020.
Haka zalika hukumar ta zayyana jahohin da aka samu karin masu cutar wadanada suka hada da:
Lagos-118 Delta-84 Ebonyi-68 FCT-56 Plateau-39 Edo-29 Katsina-21 Imo-13 Ondo-12 Adamawa-11 Osun-8 Ogun-8 Rivers-6 Kano-5 Enugu-3 Bauchi-3 Akwa Ibom-3 Kogi-1 Oyo-1 Bayelsa-1
https://twitter.com/NCDCgov/status/1277368328273760262?s=20
Bayan haka cibiyar ta bada rahoton sallamar adadin mutum 9,007 sannan kuma an samu.mutuwar mutum 565 a fadin kasar.