A karshe dai an sanar da sunayen ‘yan wasan da aka zaba da zasu lashe kyautar gwarzon dan wasan PFA na wannan shekarar.
Yayin da tauraron Manchester United Cristiano Ronaldo ya shiga sahun yan wasan, sai kuma Kevin De Bruyne wanda ya lashe kyautar a bara.
Sai kuma zakarun ‘yan wasan Liverpool guda uku, Mohammed Salah, Sadio Mane da kuma Virgil Van Dijk.