fbpx
Friday, July 1
Shadow

Cristiano Ronaldo na shirin barin Manchester United saboda taki sayen sabbin ‘yan wasa

Tauraron dan wasan gaba na kungiyar Manchester United, Cristiano Ronaldo na shirin barin kungiyar saboda taki sayen sabbin ‘yan wasa.

Ronaldo ya koma Manchester United ne a kakar bara bayan ya bar kungiyar shekaru 13 da suka gabata inda ya koma Real Madrid.

Kuma ya ciwa United kwallaye 24 a wasanni 38 daya buga mata amma duk da haka kungiyar ta shida ta kasance a gasar Firimiya.

Kuma yanzu ya bayyana masu cewa shifa zai bar kungiyar idan har basu saye sabbin ‘yan wasa ba a wannan kakar domin ko daya basu daya ba gar yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.