fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Cristiano Ronaldo na son barin Manchester United ne saboda Lionel Messi, karanta kaji dalili

Tsohon dan wasan Chelsea, Tony Cascarino ya bayyana cewa Cristiano Ronaldo na son ya bar Manchester United ne saboda Lionel Messi.

Inda yace Ronaldo na tsoron kar dan wasan Paris Saint Germain din ya kerewa masa ne a gasar zakarun Nahiyar turai sai yasa yake so ya bar Manchester.

Kuma dama Ronaldo ne gwarzon dan wasan gasar a tarihi saboda yafi kowane dan wasa zira kwallaye masu yawa a gasar ta zakarun nahiyar turai.

Amma Manchester bata cancanci buga gasar a kaka mai zuwa ba saboda haka ne yace mata ta sayar da shi kawai a wannan kakar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.