Tauraron dan wasan kwallon kafa daya lashe kyautar gwarzon duniya sau biyar, Cristiano Ronaldo ya radawa ‘yarsa suna bayan dan uwanta ya rasu.
A ranar 18 ga watan Afrilu jinjirin nasu ya mutu bayan an haife shi yayin ita kuma macen ta rayu, inda Ronaldo da budurwarsa Geogina suka bayyana hakan a Instagram.
Ronaldo da budurwar tasa sun nadawa yarinyar tasu sunan Bella Esmeralda ne, kamar yadda suka bayyana.