Rahotanni na cewa, akwai yiyuwar tauraron san kwallon Manchester United, Cristiano Ronaldo zai koma kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich.
Munich dai ta sayarwa da Barcelona babban dan wasan gabata, Robert Lewandowski.
A baya dai an rika alakanta Ronaldo da komawa Chealsea.
Saidai yanzu kuma ana tunanin zai koma Bayern Munich ne.