fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Cutar Corona Sai ta karade Nijeriya Baki Daya, Cewar Shugaban Hukumar Kula Da Cututtuka Ta Kasa

A cewar Shugaban Hukumar Kula da Dakile Cututtuka ta Kasa (NCDC), Chikwe Ihekweazu, ya baiyana cewa cutar Coronavirus zata mamaye jihohin Najeriya 36 da Abuja kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

A lokacin da ya ke magana a gidan talbijin na Channels, safiyar Alhamis, a wani shirin “Sunrise”, Chikwe ya ce, ” Coronavirus za ta bazu zuwa kowace jiha a kasar nan. inda ya kwatan ta cutar kamar cutar Zazzabin Lassa.

Sai dai ita Zazzabin Lassa ba a kulle garuruwa ba, saboda ba ta da karfi kamar Coronavirus.

Dalili kenan duk da ba a killace mutane a gida ba, mu ka yi nasarar shawo kan ta. To yanzu ana maganar Coronavirus. Cutar nan mu shirya sai ta mamaye jihohin kasar nan kalaf. Saboda babu wani dalili ko tawilin da wani zai iya kawowa, ya ce cutar ba za ta fantsama ko’ina ba.

Da ya koma kan nasarar da ake samu a yanzu, ya ce an kafa na’urorin bincike a Kano, kuma wannan ya bada damar ana samun yin bincike sosai ka cikin lokaci.

Sai dai kuma ya yi tsokaci dangane da yadda aka samu masu dauke da cutar har mutum 34 a ranar Laraba, adadin da ya ce shi ne mafi yawa da aka samu a rana daya, fum lokacin da cutar ta bazu a Najeriya.

Sama da mutum milyan biyu suka kamu da cutar a duniya. Yayin da ta kashe sama da mutum 100,000. Jihohi da dama na Najeriya na ci gaba da hana zirga-zirga, kamar yadda dokar za ta fara aiki a ranar Alhamis da dare a Kano.

A karon farko dai an samu rahoton cutar ta kashe mutum daya a Kano, bayan sama da mutum goma ne aka bada rahoton sun kamu, a birnin mafi girma a kasar, in banda Lagos.

Shugaban na Hukumar NCDC, ya ce babbar nasarar da su ke samu ita ce, “duk da fantsamar da cutar ke kara yi, su na zakulo masu dauke da ita, su na gwaji, su na killace masu cutar, kuma ana ci gaba da samun masu warkewa sosai.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.